Hukumar DSS Ta Saki Wasu Fulani Da Ta Kama

Wasu mutane 'yan ƙabilar Fulani da hukumar tsaro ta farin kaya a Najeriya DSS ta tsare sun bayyana farin ciki da ɓacin rai bayan sakin su da ta yi ranar Alhamis.

DSS ta kama mutanen uku ne yayin da suke sauka a Najeriya daga aikin Hajji a watan Yunin 2024 bisa zarge-zargen hannunsu a ayyukan garkuwa da mutane a arewacin ƙasar.

Yayin wani taron manema labarai a hedikwatarta da ke Abuja babban birnin Najeriya, DSS ta gabatar da Rabiu Alhaji Bello, da Umar Ibrahim, da Bammo Jajo Sarki duka 'yan jihar Kwara da ke tsakiyar ƙasar.

Hukumar ta ce ta kammala bincike kansu kuma ba ta same su da laifin komai ba, abin da ya sa ta bai wa kowannensu kyautar naira miliyan ɗaya.

Post a Comment

Previous Post Next Post