A daren ranar Litinin ne ƙungiyar ƙasashen yankin Sahel ta AES, wadda ta ƙunshi Burkina Faso da Mali da Jamhuriyar Nijar suka fitar da sanarwar yin tir da abin da suka kira keta musu sararin samaniya da wani jirgin sojin Najeriya ya yi ba bisa ƙ'aida ba.
An bayyana cewa jirgin ƙirar C-130 na rundunar sojin Najeriya ya sauka ne a garin Bobo Dioulasso da ke ƙasar ta Burkina Faso, a ranar Litinin.A cewar sanarwar da ƙungiyar AES ta fitar, matakin jirgin na Najeriya ya saɓa ka'idojin ƙasashen duniya, sannan suna daukar irin wannan a matsayin "laifi kan ƴancin ƙasa".
Sai dai jim kaɗan bayan haka, hukumomin Najeriya sun fitar da nasu bayanin inda suka ce "tangarɗar na'ura ce ta sanya jirgin ya sauka a ƙasar ta Burkina Faso".