Ko Me Zai Faru Ga Wanda Bai Yi TIN Ba?

Da alama ƴan Najeriya sun shiga ruɗu dangane da rashin sanin abin da zai faru da su daga ranar 1 ga watan Janairun 2025 lokacin da sabuwar dokar haraji ta ƙasar za ta fara aiki.

Matakin farko na wannan haraji shi ne cewa dole ne duk ɗan Najeriya da ke hulɗa da asusun banki ya mallaki lambar TIN wadda ta nan ne za a san wane ne ya kamata ya biya harajin sannan kuma nawa zai biya.

Irin wannan ruɗani dai ya fara ne a watan Satumbar 2025 ɗin nan lokacin da gwamnatin ƙasar ta fitar da sanarwar wajabcin mallakar lambobin na TIN ga ƴan ƙasa domin samun damar amfani da asusunsu na bankunan a nan gaba.

Shugaban kwamitin shugaban ƙasa kan gyaran fuska ga sha'anin kuɗi da haraji na Najeriya, Taiwo Oyedele ne ya sanar da hakan da farko to amma daga baya sai ya fayyace abin da yake nufi bayan al'amarin ya tayar da ƙura.

"Wajabcin mallakar wannan lambar ta taƙaitu ne ga mutane da kamfanonin da ya kamata su biya haraji - ba ta shafi ƴan Najeriyar da abin da suke samu bai kai a cire musu haraji daga ciki ba," in ji Oyedele.

Shin mece ce ita wannan lambar? Kuma yaya ake samun ta? BBC ta yi nazari kamar haka:

Post a Comment

Previous Post Next Post