Zazzafar cacar-baki ta kaure tsakanin Ministan Abuja, Nyesom Wike, da Sakataren Jam'iyyar APC, Ajibola Bashiru, lamarin da ya kai ga sakataren jam'iyyar kiran Wike ya sauka daga muƙaminsa na minista, bisa hujjar cewa ba ɗan jam'iyyar APC ba ne.
Lamarin na zuwa ne bayan Wike ya gargaɗi sakataren ya tsame hannunsa daga siyasar jihar Ribas, saboda sanarwar da APC ta fitar cewa Gwamna Siminalayi Fubara ne jagora kuma shugaban jam'iyyar mai mulki a jihar.Rikicin ya faro ne tun bayan ziyarar da sakataren APCn da tawagarsa suka kai wa Gwamna Siminalayi Fubara a jihar Ribas, inda daga bisani Bashiru ya sake jaddada tsarin jam'iyyar cewa kowane gwamna shi ne jagoran jam'iyyar a jiharsa.
Sakataren ya ce Nyesom Wike ba ɗan APC ba ne, don haka ba shi da hurumin tsoma baki a harkokin jam'iyyar, tare da shawartarsa da ya sauka daga muƙamin minista kuma ya daina halartar taron Majalisar Zartarwar ƙasar.
Sai dai a martaninsa, Nyesom Wike - wanda tsohon gwamnan jihar ta Ribas ne kuma tsohon mai gida na siyasa ga Gwamna Fubara - yayin wani rangadi da ya kai ƙaramar hukumar Gokana ta jihar Ribas ɗin, ya buƙaci sakataren jam'iyyar da ya tsame hannunsa daga siyasar jihar.
A watan Disamban da ya gabata ne dai Gwamnan jihar Ribas, Similanayi Fubara ya fice daga jam'iyyar PDP zuwa APC mai mulki, a wani mataki da wasu ke ganin tamkar shatale ƙafa ne ga Wike.