Gwamnatin Venezuela ta zafafa kamen da take yi wa ƴan'adawar siyasa bayan hamɓarar da shugaban ƙasar, Nicolas Maduro tare da kama shi.
Jami'an ƴansandan riƙe da makamai sun zafafa sintiri a kan titunan Caracas, babban birnin ƙasar.Ministan Shari'ar ƙasar, Diosdado Cabello, ya wallafa wani hoto da ya ɗauka da jami'an tsaron a shafinsa ranar Litinin da daddare.
A ɗaya daga cikin bidiyoyin da ya wallafa an jiyo jami'an tsaron na cewa ''biyayya koyaushe, bijirewa babu''.
Rahotonni na cewa ƙungiyoyin masu tayar da ƙayar baya - bisa umarnin gwamnati - na cusguna wa mutane da ke murnar hamɓarar da Maduro a wani harin Amurka.