An ci gaba da zanga-zangar ƙin jinin gwamnati a Tehran, babban birnin ƙasar Iran.
Dandazon mutane ne suka yi zaman dirshan a babbar kasuwar Bazaar da ke birnin, suna rera waƙoƙin nuna adawa ga jagoran addinin ƙasar, Ayatollah Ali Khamenei.An samu arangama tsakanin masu zanga-zangar da ƴansanda, inda jami'an suka riƙa harba hayaƙi mai sa hawaye tare da rufe wasu yankunan kasuwar mai tarihi.
Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan'adam ta ƙasar ta ce aƙalla mutum 35 ciki har da jami'an tsaro biyu aka kashe tun fara zanga-zangar kwanaki 10 da suka gabata.
Wata ƙungiyar ta ce fiye da mutum 1200 aka tsare yayin da zanga-zangar ta bazu zuwa lardunan ƙasar 27 cikin 37.