Shugaban Venezuela Nicolas Maduro ya bayyana wa kotun New York cewa shi mutum ne mai nagarta, kuma bai aikata laifin komai da ya cancanci a tsare shi a Amurka ba.
Maduro ya bayyana haka ne a gaban kotu, inda ya ce, "ban aikata laifi ba. Ni mutumin kirki ne, kuma shugaban ƙasata," in ji shi kamar yadda tafinta ya fassara.Maduro ya bayyana haka ne a matsayin martani bayan an zayyana masa tuhume-tuhume guda huɗu da ake zargin ya aikata.
Sai dai ya musanta aikata duka laifukan, sannan matarsa ma ta musanta aikata laifuka.
Laifukan da ake tuhumarsa da su sun haɗa da safarar miyagun ƙwayoyi da mallakar makamai da sauransu.