An fara gudanar da bincike kan yadda ɗaya daga cikin tayar jirgin British Airways ya ɓalle ya faɗi ƙasa, jim kaɗan bayan tashi daga filin jirgin sama na Las Vegas.
An ɗauki yadda lamarin ya faru kai-tsaye, inda aka yi ta yaɗa bidiyon a kafofin sada zumunta.Jirgin na Airbus A350 ya samu damar ci gaba da tafiya, kuma ya sauka ba tare da wata matsala ba a birnin Landan sa'o'i tara bayan faruwar lamarin.
Wata sanarwa da kamfanin jirgin ya fitar, ya ce yana mayar da hankali sosai kan kariya da kuma tsaro a dukkan ayyukansa - ya kuma ce zai bai wa hukumomi haɗin-kai a binciken su.