Duk da cewa fadar shugaban Najeriya ta fitar da bayani domin yayyafa ruwa kan muhawarar da ake tafkawa game da tuntuɓen da shugaban ƙasar, Bola Tinubu ya yi a ƙasar Turkiyya, lamarin na ci gaba da tayar da ƙura.
Tinubu mai shekara 73 ya yi tuntuɓe ne ya faɗi a daidai lokacin da ake masa bikin tarbar ban-girma a Ankara, babban birnin ƙasar Turkiyya.Tun da farko, Tinubu ya ratsa ta tsakiyar sojoji da suka yi masa faretin girmamawa da kuma manyan jami'an gwamnati da suka tarbe shi.
Sai dai suna cikin tafiya ne tare da Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan, kwatsam sai ya yi tuntuɓe ya faɗi.
Bidiyon mai kimamin daƙiƙa 45 ya nuna mutane suna ƙoƙarin ɗaga shi, kafin daga bisani aka gan su tare da shugaban na Turkiya suna ci gaba da tafiya.
Tuni dai masu magana da yawun shugaban suka yi watsi da batun, inda suka nanata cewa lafiyarsa ƙalau, sannan suka ce tuntuɓe ne kawai, kuma tuni ya ci gaba da gudanar da abubuwan da suka kai shi ƙasar.
Babu dai wata alamar rauni da aka gani a tattare da Tinubun domin ya miƙe ya ci gaba da tafiya, sannan mai magana da yawunsa, Sunday Dare ya ce Tinubu ya ci gaba da tattaunawa da ƙulla yarjejeniyoyin da suka kai shi ƙasar.
Da yake bayani kan haƙiƙanin abin da ya faru, mai magana da yawun shugaban Najeriya Bayo Onanuga ya ce Tinubu ya taka wani ƙarfe da ke ƙasa a lokacin da yake tafiya.
Wannan ƙarfen da ya taka ne ya sa ya ɗan yi tuntuɓen tafiya," in ji Bayo a wata sanarwa da ya fitar.
Ya ƙara da cewa babu wata matsala, "sai dai masu neman abin magana ne a kusan kowane irin abin da ya faru. Kawai tuntuɓe ya yi ba wani abu ba, muna godiya ga Allah ba faɗuwa ya yi ba," in ji shi.
Sai dai duk da haka mutane sun ci gaba da muhawara kan batun a shafukan sada zumunta.
A nasa bayanin, Sanata Shehu Sani ya ce lamarin ya nuna cewa shugaban mutum ne kamar kowa.
Shi ma wani mai magana da yawun shugaban na Najeriya, Sunday Dare, ya wallafa a shafinsa na X, inda ya ce Tinubu na cikin ƙoshin lafiya, kuma ya ci gaba da gudanar da aikace-aikacen da suka kai shi kamar yadda aka tsara.
"Bayan tarba ta musamman da aka yi masa a Ankara, ya samu damar tattaunawa da shugaban Turkiyya da sauran jami'an gwamnati na Najeriya da na ƙasar Turkiyya," in ji shi a sanarwar.