An shiga sabon yanayi na tashin hankali a Siriya bayan da sojojin gwamnati suka fara kutsawa birnin Hasakah, lamarin da ke jefa yarjejeniyar tsagaita wuta cikin barazana mai tsanani. Rahotanni daga yankin na nuna cewa ana jin ƙarar harbe-harbe da motsin manyan motocin soji duk da iƙirarin cewa an cimma tsagaita wuta.
Majiyoyi sun ce tsagaita wutar da aka amince da ita na zuwa ne a karkashin matsin lamba, inda bangarori ke zargin juna da karya sharuddan yarjejeniyar. Ƙungiyoyin da ke iko da wasu sassan Hasakah sun bayyana fargaba cewa wannan matakin na sojojin gwamnati na iya janyo barkewar faɗa mai tsanani.
Mazauna yankin sun fara ficewa daga gidajensu, yayin da wasu ke neman mafaka a yankunan da suke ganin sun fi aminci. Hukumomin agaji sun ce akwai fargabar barkewar rikicin jin kai, musamman idan aka ci gaba da kutse da artabu a cikin birnin.
A bangaren gwamnati kuwa, jami’an tsaro sun ce matakin da suka dauka na da nasaba da kare tsaro da dawo da ikon gwamnati, suna musanta zargin karya tsagaita wuta. Sai dai masu lura da al’amuran Siriya na ganin halin da ake ciki na iya kara dagula rikicin da ya dade yana addabar kasar, tare da kawo cikas ga kokarin sulhu.