Abin da ya sa muka amince da ɓangaren Wike na PDP - INEC

Hukumar zaɓen Najeriya ta bayyana dalilin da ya sa ta amince da shugabancin riƙon ƙwarya da ɓangare Nyesom Wike ya samar a jam'iyyar PDP. 

INEC ta ce tana biyayya ne ga doka da hukuncin kotu kan duk wani mataki da ta ke ɗauka, ko dai a kan jam'iyyun siyasa ko ƴan takara ko kuma rikicin cikin gida na jam'iyyun Najeriya, kamar yadda kundin mulkin ƙasa ya yi tanadi.

Bayanin hukumar INEC na zuwa ne bayan sabon rikicin shugabanci da ya kunno kai a cikin jam'iyyar PDP, inda ake jayayya tsakanin shugabanci ƙarƙarshin Kabiru Tanimu Turaki, da kuma shugabancin riƙon ƙwarya ƙarƙashin Mohammed Abdulrahman, mai samun goyon bayan ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike

PDP ta zaɓi Tanimu Turaki a matsayin shugabanta na ƙasa ne a wajen babban taron da ta yi cikin watan Nuwamban bara a birnin Ibadan na jihar Oyo, duk da cewa tun da farko an gudanar da taron ne cikin jayayya da iƙirarin umarnin kotu masu karo da juna tsakanin ƴaƴan jam'iyyar.

A ranar Juma'a, 30 ga watan Janairun 2026 kuma wata babbar kotun tarayya a Ibadan, babban birnin jihar Oyo, ta rusa shugabancin jam'iyyar PDP ƙarƙashin jagorancin Kabiru Tanimu Turaki.

Kotun ta ce an gudanar da babbn taron PDP na Ibadan ne a bisa yi wa umarnin kotu karan tsaye, domin haka duk wata matsaya ko hukuncin da aka yanke a yayin taron ya saɓa doka kuma ba zai taɓa zama gaskiya.

Har ila yau, kotun ta amince da ɓangaren shugabancin riƙon ƙwarya na Mohammed Abdulrahman a matsayin shugaban jam'iyyar, har sai an gudanar da babban taron jam'iyyar.

A wata hira da BBC, ɗaya daga cikin masu magana da yawun hukumar INEC, Zainab Aminu ta ce hukumar ta ɗauki matakin ne saboda biyayya ga umarnin da kotun ta bayar game da dambarwar shugabancin PDP.

Post a Comment

Previous Post Next Post