Adadin mutanen da suka mutu sakamakon wata mummunar guguwar cyclone da ta afkawa Madagascar ya ƙaru zuwa 38, yayin da kusan mutum 12,000 suka rasa matsugunansu, a cewar hukumomi.
Guguwar ta haddasa ambaliyar ruwa, rushewar gidaje da lalacewar amfanin gona, lamarin da ya jefa dubban iyalai cikin mawuyacin hali. Ma’aikatan agaji na cikin ƙoƙarin kai kayan taimako ga yankunan da abin ya fi shafa, musamman a sassan da hanyoyi suka lalace ko suka zama marasa amfani.
A halin yanzu, ƙasar makwabciya ta Mozambique na shirin karɓar guguwar yayin da hukumomin ta ke faɗakar da jama’a su koma wuraren tsaro. An tura jami’an ceto tare da shirya matsugunan wucin gadi domin rage asarar rayuka da dukiyoyi.
Yankin Kudancin Afirka na yawan fuskantar guguwar cyclone a wannan lokaci na shekara, amma masana na gargadin cewa canjin yanayi na ƙara tsananta ƙarfin guguwar da yawan aukuwarta.