Wata kotu a Amurka ta yanke wa fitaccen madugun adawar Sudan ta Kudu hukuncin ɗaurin kusan shekara 45 a gidan yari, saboda samunsa da laifin shirin kifar da gwamnatin ƙasarsa.
An samu Peter Bijar Ajak - ƙwararren masanin tattalin arziki - wanda ya yi karatu a jami'o'in Cambridge da Harvard, da ke zaune a kusa da birnin Washington - da laifin safarar makamai.Jami'an Amurka sun ce Mista Ajak ya shirya saye makamai na dala miliyan huɗu daga Am jurka domin kai su Sudan ta Kudu don raba su ga ƙungiyoyin mayaƙa, domin cimma burinsa na zama shugaban ƙasar.
An kam Ajak a shekarar 2018 a Sudan ta Kudu, inda aka tsare a gidan yari na wata 18.