Kurar rikici ta fara turnuƙewa a jam'iyyar APC mai mulki a jihar Kano, da ke arewacin Najeriya, makonni bayan sauyin sheƙar gwamna Abba Kabir Yusuf.
An fara ganin ƙurar ne a tarukan haɗa kan 'ya'yan jam'iyyar APC tsoffi da sabbi a cikin wasu ƙananan hukumomin jihar.Shugabancin APC ne ya ba da umarnin gudanar da tarukan masu ruwa da tsaki na jam'iyyar a wani mataki na ɗinke duk wata ɓaraka gabanin babban zaɓen jam'iyyar da ke tafe.
Dama dai tun da farko masana siyasa a Najeriya sun yi hasashen samun rikici a tsakanin ƴaƴan jam'iyyar APC musamman bayan shigowar gwamna Abba Kabir Yusuf.
Rahotanni na cewa an samu musayar yawu da cecekuce a yayin taron masu ruwa da tsaki a matakin kananan hukumomi.
Na baya-bayan nan shi ne taruka biyu da aka yi a karamar hukumar Kano Municipal inda ɓangaren da ke biyayya ga tsohon gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ƙarƙashin jagorancin Muntari Ishaq Yakasai da Baffa Babba Dan Agundi da Injiniya Sagir Koki, suka yi nasu taron.
Kodayake koda BBC ta tuntuni Baffa Babba Dan Agundi, kan dalilin yin nasu taron, ya shaida ma ta cewa ba shi da masaniya a kan taron, sannan kuma duk wanda ke da ruwa da tsaki a jam'iyyarsu ta APC an gayyace shi sai dai wanda bai samu halarta ba.
Ya ce," Mu ba mu da matsala duk wanda zai kira taro don haɗin kan jam'iyya za mu je sai dai idan ba a sanar da mu ba."