Kitso ga mata, da kuma aski ga maza, wani abu ne tamkar wajibi - domin tabbatar da tsafta, kiwin lafiya da kuma ado.
Mako-mako ko wata-wata ko kasa da haka, kowa na da lokacin da yake dauka kafin ya je a rangada masa aski ko kuma a rangada mata kitso.
Domin kuwa wadamnam abubuwa biyu, idan har ba a dauki matakan da suka dace ba wajen tabbatar da tsafta da kuma kare lafiya, masana na cewa hanyoyi ne na yada cutuka cikin sauri.
A yawancin lokuta, mutane sun fi damuwa da irin salo ko kyawun da za su fito da shi, ba tare da la'akari da irin kayan aikin da ake amfani da su ba.
Duk da cewa zamani ya zo da kayan aiki na zamani wajen aski ko kitso, to amma hadarinsu wajen yada cutuka kusan iri daya ne da reza, almakashi, mataji ko kuma tsinken tsifa da ake amfani da su tun kaka da kakanni.
Hadarin kamuwa da cutuka a wurin aski ko kitso ya fi kamari ne idan ba a daukar matakan da suka dace wajen tsaftace kayan aiki.
Wasu lokutan ma, ana samun ƙananan raunuka yayin aski ko kitso kamar yanka a fatan kai da sauransu wanda mutane ba su cika lura da shi ba.