Jihar Zamfara ta shiga cikin jimami a ranar Juma’a bayan da wasu ‘yan bindiga suka kashe aƙalla mutane 50 a ƙauyen Dutsin Dan Ajiya da ke Ƙaramar Hukumar Anka ta jihar.
An ga gawarwakin mamatan sanye da fararen likkafani ana shirin yi musu jana’izar gama-gari, kamar yadda wani bidiyo da Saturday PUNCH ta gani ya nuna.Wani mazaunin ƙauyen, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya bayyana cewa maharan ɗauke da makamai masu ƙarfi sun kai harin ne a daren Alhamis, inda suka riƙa harbe-harbe ba kakkautawa.
Ya ƙara da cewa ‘yan bindigar sun toshe dukkan hanyoyin shiga da fita daga ƙauyen domin hana jama’a tserewa.
A cewarsa, “Bayan sun rufe hanyoyin, sai suka fara harbin duk wanda suka gani, lamarin da ya sa jama’a suka ruga suna neman mafaka.
“Bayan harin, mun gano cewa mutane 30 sun mutu nan take; wasu sun jikkata, yayin da wasu da dama suka ɓace kuma ba a san inda suke ba.”
Saturday PUNCH ta ruwaito cewa maharan sun kuma sace mutane da dama a yayin harin, wanda ya ɗauki tsawon dare har zuwa wayewar garin Juma’a.
Sai dai kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ce adadin waɗanda aka kashe ya kai aƙalla 50.
Ɗan majalisar da ke wakiltar mazaɓar Bukkuyum ta Kudu, Hamisu Faru, ya shaida wa kamfanin dillancin labaran cewa maharan sun fara kai harin da misalin ƙarfe 5:00 na yammacin Alhamis har zuwa kusan ƙarfe 3:30 na asubahin Juma’a, inda suka ƙone gine-gine tare da harbin mazauna da suka yi yunƙurin tserewa.
“Sun kasance suna kai hari daga ƙauye zuwa ƙauye… suna barin aƙalla mutane 50 a mace,” in ji Faru.
Wani mazaunin ƙauyen mai shekaru 41, Abdullahi Sani, ya ce mutum uku daga cikin iyalansa sun mutu a harin.
Ya ce, “Babu wanda ya yi barci jiya; duk muna cikin raɗaɗi da jimami.”
A cewarsa, mazauna ƙauyen sun sanar da jami’an tsaro da hukumomin yankin tun lokacin da suka hango fiye da babura 150 ɗauke da maharan, amma ba su samu wani taimako ba.
Hakazalika, a ranar 13 ga Fabrairu, 2026, wasu ‘yan ta’addan Lakurawa sun kai hari a ƙauyen Maganho da ke Ƙaramar Hukumar Tangaza a Jihar Sokoto, inda suka kashe mutane biyar tare da kwashe dabbobi masu yawa mallakin manoma.
Haka kuma, a Jihar Katsina, ‘yan bindiga sun kashe mutane 21 a garin Doma da ke Ƙaramar Hukumar Faskari a ranar 3 ga Fabrairu. Harin ya rusa yarjejeniyar zaman lafiya ta watanni shida da al’ummar yankin suka cimma da maharan.
Da yake mayar da martani kan lamarin, Daraktan Zartarwa na gidauniyar Foundation for Peace Professionals, Abdulrazaq Hamzat, ya musanta cewa sabbin kashe-kashen na nuni da dawowar sabon rikici, yana mai cewa abin da ke faruwa ci gaba ne na matsalar tsaro da ta daɗe tana addabar yankin.