Majalisar Dokokin Amurka ta Zargi Kwankwaso

Ƴan majalisar wakilan Amurka sun gabatar da wani ƙuduri a zauren majalisar wanda ya ƙunshi rahoto kan kwamitin bincike game da zargin cin zarafin kiristoci da cusguna musu a Najeriya.

Haka nan rahoton ya bayar da shawarwari kan matakan da suka kamata Amurkar ta ɗauka wajen magance matsalar.

Wasu ƴan majalisa na jam'iyyar Republican ne suka gabatar da ƙudurin, wanda a ciki suke kira ga sakataren harkokin wajen Amurka kan ya ayyana wasu ƙungiyoyi ƴan bindiga a matsayin ƴan ta'adda, sannan kuma a sanya takunkumi kan wasu ƴan Najeriya.

Sauran matakan da ƙudurin ke son a ɗauka su ne hana wadanda ake zargi da hannu a 'cin zarafin' kiristoci shiga Amurka da ƙwace kadarorinsu.

Cikin waɗanda sunansu ya fito ɓaro-ɓaro a ƙudurin akwai tsohon gwamnan Kano Rabiu Musa Kwankwaso da ƙungiyar Miyetti Alla Kautal Hore da Miyetti Allah Cattle Breeders (MACBAN) da kuma abin da ƙudurin ya kira "ƙungiyoyin Fulani masu ɗauke da makamai a Najeriya."

Ƙudurin, wanda aka yi wa laƙabi da 'Nigeria Religious Freedom and Accountability Act of 2026' an gabatar da shi ne da nufin shawo kan zargin da tun farko Amurka ta yi na cewa ana kashe kiristoci a Najeriya kawai saboda addininsu.

Gwamnatin Najeriya dai ta sha musanta zargin musguna wa Kiristoci a ƙasar, inda ta ce "rashin tsaro ya shafi al'umma a ƙasar ba tare da la'akari da bambancin addini ba".

Tuni dai shugaban Amurka Donald Trump ya ayyana Najeriya a matsayin ƙasar da ake da damuwa a kanta.

Post a Comment

Previous Post Next Post