TAMBAYA TA 3265
Assalama alaikum wa rahamatullah Malam don Allah ina son a min bayanin yadda Annabi ﷺ yake yin sallahr shafa'i da wuturi please da karatun da komai ma please🙏
AMSA
Wa alaikis salam wa rahmatulLahi wa barakatuhu.
Akwai riwayoyi mabambanta daga Sahabbai daban-daban dangane da
siffar shafa'i da wutrinsa ﷺ
amma dai ga wasu bayanai nan a takaice :
Ibnu Maajah ya ruwaito daga Sayyiduna Abdullahi bn Umar
(radhiyalLahu anhuma) cewa shi ya kasance yakan sallaci shafa'i da wutiri
acikin raka'a uku ne. Yakan raba tsakaninsu da sallama. Kuma shi Abdullahi din
ya ce "Haka ya ga Manzon Allah ﷺ
yana aikatawa".
Al Hafiz Ibnu Hajr ya ce isnadin wannan hadisin mai karfi ne. (Aduba
Fat'hul Baariy sharhin Bukhariy juzu'i na 2 shafi na 482).
Wannan hadisin da wasu ire-irwnsa suna tabbatar da cewa abinda
ake nufi da shafa'i din nan shine 'BIYUNTAWA' ma'ana duk wata lamba wacce za'a
iya rabata gida biyu acikin lissafin kidaya, kamar biyu, hudu, shida, takwas,
da sauransu.
Amma shi kuwa wutiri ma'anarsa ita ce 'MARA' Wato kamar daya ko
uku ko biyar ko bakwai ko tara. Kamar yadda hadisai ingantattu suka nuna cewar
Manzon Allah ﷺ
yakan sallaci wutiri raka'a daya ko uku ko biyar ko tara. (kowacce siffah ta
inganta)..
Amma Maluman da suka zabi yin wutiri da raka'a guda sun dogara
ne da wasu hadisai ingantattu kamar hadisin nan da Imamul Bukhariy da Muslim
suka riwaito Manzon Allah ﷺ
yana cewa :
"Sallar dare biyu-biyu ake yinta (wato duk raka'a biyu a
yi sallama) Idan 'dayanku yaji tsoron wayewar gari, sai ya sallaci raka'a guda
wacce zata zamar masa wutirin abinda.ya riga ya sallata"
Da kuma daya hadisin da Manzon Allah ﷺ
ya ce : "Wutiri raka'a guda ne a karshen dare".
YADDA AKE YIN SHAFA'I : Idan raka'a biyu zakiyi, to siffar da
aka ruwaito daga Manzon Allah ﷺ
ita ce ki karanta fatiha da suratul A'ala (Sabbihisma Robbikal A'ala) a raka'ar
farko.
A raka'a ta biyu kuma fatiha da suratul Kafirun (Qul Ya Ayyuhal
Kafiroon).
Sai ki zauna kiyi tahiya (attahiyyatu) kiyi sallama sannan ki
mike kiyi wutiri.
SHI KUMA WUTIRIN: Idan mai raka'a guda din zakiyi, sai ki
karanta fatiha da Qul huwal Lahu da Falaqi da Nasi. Kiyi tahiyah kiyi sallama shi
ke nan.
Idan kuma wutiri mai raka'a uku zakiyi ko biyar, zaki yisu ne
duk raka'o'in ba tare da kin zauna ba, sai a raka'ar karshe ne zaki zauna kiyi
tahiyyah kiyi sallama. (Kamar yadda Imamun Nisa'iy da Baihaqiy suka riwaito
daga Nana A'isha (radhiyalLahu anha) tace haka Annabi ﷺ
yake yi. Da kuma riwayar Imamu Muslim shima daga Nana A'isha.
An fi son yin shafa'i da wutiri a karshen dare idan har mutum
yasan zai farka akan lokaci. Amma idan mutum yasan yana da nauyin barci an so
yayi shafa'i da wutirinsa kafin ya kwanta barci.
WALLAHU A'ALAM.
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
