𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu Alaikum.. Allah ya saka ma malam da alheri. Malam dan Allah inaso a fada min addu'an da zan yawaita yi a duk lokacin da gabana ya fadi.. Ina yawan faduwan gaba.. Nagode.
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa alaikis salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.
Akwai addu'o'i da yawan gaske waɗanda zaki iya yinsu a irin
wannan yanayin tsorata ko firgita ko faduwar gaba.
Ga wasu nan:
ﺃَﻋُﻮﺫُ
ﺑِﻜَﻠِﻤَﺎﺕِ ﺍﻟﻠَّﻪِ ﺍﻟﺘَّﺎﻣَّﺎﺕِ ﻣِﻦْ ﻏَﻀَﺒِﻪِ ﻭَﻋِﻘَﺎﺑِﻪِ، ﻭَﺷَﺮِّ ﻋِﺒَﺎﺩِﻩِ، ﻭَﻣِﻦْ
ﻫَﻤَﺰَﺍﺕِ ﺍﻟﺸَّﻴَﺎﻃِﻴﻦِ ﻭَﺃَﻥْ ﻳَﺤْﻀُﺮُﻭﻥِ
'A'oodhu bikalimaatil Laahit-taammaati min ghadhabihi wa
'iqaabihi, wa sharri 'ibaadihi, wa min hamazaatish shayaateeni wa 'an
yahdhuroon.
FA'IDAR YINTA: Duk lokacin da zakiyi barci ki rika karanta ta,
bayan addu'o'in da kikeyi. Qafa uku ake karantawa. Ko da dare ko da rana, ko
kuma duk lokacin da kika ji faduwar gaba ko razana. Kuma ana tofa wa Qananan
yara domin magance sharrin kambun ido, ko razana ko miyagun mafarkai.
ﺃَﻋُﻮﺫُ
ﺑﻜَﻠِﻤَﺎﺕِ ﺍﻟﻠَّﻪِ ﺍﻟﺘَّﺎﻣَّﺎﺕِ ﺍﻟَّﺘِﻲ ﻟَﺎ ﻳُﺠَﺎﻭِﺯُﻫُﻦَّ ﺑَﺮٌّ ﻭﻟَﺎ ﻓَﺎﺟِﺮٌ ﻣِﻦْ
ﺷّﺮِّ ﻣَﺎ ﺧَﻠﻖَ، ﻭﺑَﺮَﺃَ ﻭَﺫَﺭَﺃَ، ﻭﻣِﻦْ ﺷَﺮِّ ﻣَﺎ ﻳَﻨْﺰِﻝُ ﻣِﻦَ ﺍﻟﺴَّﻤَﺎﺀِ، ﻭِﻣﻦْ
ﺷَﺮِّ ﻣَﺎ ﻳَﻌْﺮُﺝُ ﻓِﻴﻬَﺎ، ﻭﻣِﻦْ ﺷَﺮِّ ﻣَﺎ ﺫَﺭَﺃَ ﻓِﻲ ﺍﻷَﺭْﺽِ، ﻭﻣِﻦْ ﺷَﺮِّ ﻣَﺎ ﻳَﺨْﺮُﺝُ
ﻣِﻨْﻬَﺎ، ﻭَﻣﻦْ ﺷَﺮِّ ﻓِﺘَﻦِ ﺍﻟﻠَّﻴْﻞِ ﻭَﺍﻟﻨَّﻬَﺎﺭِ، ﻭﻣِﻦْ ﺷَﺮِّ ﻛُﻞِّ ﻃَﺎﺭِﻕٍ ﺇِﻟَّﺎ
ﻃَﺎﺭِﻗﺎً ﻳَﻄْﺮُﻕُ ﺑْﺨَﻴْﺮٍ ﻳَﺎ ﺭَﺣْﻤَﻦُ
'A'oodhu bikalimaatil Laahit-taammaati Allatee laa
yujaawizuhunna barrun wa laa faajirun min sharri maa khalaqa, wa bara'a wa dhara'a,
wa min sharri maa yanzilu minas samaa'i, wa min sharri maa ya'aruju feehaa, wa
min sharri maa dhara'a fil-'ardhi, wa min sharri ma yakhruju minhaa, wa min
sharri fitanil-layli wannahaari, wa min sharri kulli taariqin 'illaa taariqan
yatruqu bikhayrin yaa Rahmaan.
FA'IDARTA: Qafa ɗaya ake karantawa, Kuma magani ce akan dukkan
matsalolin shaiɗanun Aljanu da mutane komai Qarfinsu, komai yawansu. Kuma tana
magance sharrin fajirai da matsafa da dukkan Azzalumai da mahassada.
WALLAHU A'ALAM.
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance damu cikin
wannan group domin Fadakarwa...
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
