Masussuka Ya Tsayar Da Hujja Ma Kansa

Tun a semister ta farko, a Fuculty na Hadisi, a Jami'ar Madina, aka karantar da mu darasin tarihin rubuta Hadisan Annabi (saw). Wato darasin "تدوين السنة". A nan aka karantar da mu tushen fara tattatara Hadisi da rubuta shi.

Lallai duk wanda bai san wannan ilimi ba, to lallai da wuri za a ruɗa shi, game da Hadisan Annabi (saw). Kuma na tabbatar da haka daga Masussuka, na gane bai san miye Hadisi ba!

Bai san miye rubuta Hadisi da wallafa shi ba!

Shi a zatonsa, farkon Hadisi shi ne daga lokacin da su Imamu Malik suka fara wallafa littatafan Hadisai.

To ka ga wannan jahilci ne "Murakkabi".

To, asali an shar'anta mana yin "Mujadala" ta hanya mafi kyau da waɗanda suka kauce hanyar gaskiya.

Da ma ita Mujadala tambaya da amsa ce. Bayan haka kuma akwai ƙa'idoji da sharuɗa da aka gindaya don isa ga gaskiya.

Daga cikin muhimman ƙa'idojin Mujadalar akwai; sanya wata ƙa'ada wacce za ta zama Alƙali mai hukunci.

To Alkali a tsakaninmu da "shaiɗaniyyun" ƴan tatsine shi ne Alƙur'ani, saboda shi ne kaɗai ya haɗa mu da su.

Wannan ya sa aka so Masussuka ya tabbatar da ingancinsa Aƙidarsa daga cikin Alƙur'ani kaɗai.

To amma bisa amsa da ya bayar ga tambayar farko, sai ya kasa ba da amsa daga Alƙur'ani, sai ya fara kame - kame, ƙarshe ya tiƙe a kafa hujja da Hadisin Annabi (saw), wato aikinsa. Inda ya ce: sun gane Salloli biyar ne, da yawan raka'o'in kowace Sallah, da yadda ake yin Sallolin gaba ɗaya daga Annabi (saw), kamar yadda Sahabbai suka ga yadda Annabi (saw) yake yi, suka koya daga gare shi, Tabi'ai suka koya daga Sahabbai, Tabi'u daga Tabi'ai, Taba'u daga Tabi'u,,, haka nan har abin ya iso gare mu. Wato dai Annabi (saw) ne ya koyar da Sallah, da dukkan abin da ya shafe ta, na yawan sallolin, da siffarsu da "kaifiyya", da kuma yawan raka'o'i. Don haka wannan shi ake kira: "Riwaya Mutawatira" (النقل المتواتر), ko "Hadisi Mutawatiri", ko "Sunna Mutawatira"...

To da wannan za ka fahimci Masussuka ya tabbatar da Hadisi, amma ba tare da ya sani ba.

Kuma wani abu shi ne; Masussuka bai ma fahimci miye Hadisi ba!

Ai Hadisi shi ne; "Dukkan abin da aka jingina wa Annabi (saw); na magana, ko aiki, ko abin da aka yi ya tabbatar, ko bai yi inkari ba, ko siffarsa ta halitta, ko ta hali da ɗabi'a".

Amma shi Masussuka ya ɗauka wallafa littatafan Hadisai ne kawai Hadisi.

Ba ya banbance Hadisi da "dawwana" Hadisi, wato rubuta shi da wallafawa a littatafai. Bai san cewa; tun kafin su Imamu Malik su wallafa littatafan Hadisi, Hadisan suna nan, ana naƙalto su, ana ruwaito su, ana aiki da su.

Ai su su Imamu Malik, ba su suka ƙirƙiri Hadisan ba. Ba kuma su suka fara jin su daga Annabi (saw) ba. Kai, hatta rubutawa da wallafawar, ba su suka fara ba! A'a, da ma Hadisan suna nan, ana ruwaito su da baki, ko kuma a rubuce, amma ba a tattare waje guda ba. Don haka abin da su Imamu Malik suka yi shi ne tattara Hadisan wuri guda, da wallafa su a littafai, da jera su babi-babi.

Saboda haka, tun da ba Mujadala ce tsararriya ba, wato wacce aka tsara ta a wuri ɗaya, duka ɓangarori biyu su halarta, to mutane ne za su yi hukunci.

Don haka lallai duk wanda ya saurari Masussuka zai ji amsoshin da ya bayar ba su gamsar ba. Hasali ma ya tsayar da hujja ne ma kansa, tun a amsa tambayar farko ya yi iƙrari da Hadisi da Sunna ba tare da ya sani ba.

Dr. Aliyu Muh'd Sani (H)

Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

Masussuka Da Kabir Gombe

Abu-Ubaida Sani

I provide language services such as translation, transcription, proofreading, interpretation, etc in the Hausa language. I also outsource in Pidgin, Yoruba, Igbo, Fulah, and Kanuri. Contact me through email: abuubaidasani5@gmail.com or WhatsApp: +2348133529736

Post a Comment

Previous Post Next Post