Taƙaitaccen Lissafin Tarin Asarar Da Aka Tafka A Kasuwannin Kano Cikin Shekaru Goma Daga 2016-2026

JERIN GOBARA DA SUKA FARU A KASUWANNIN KANO DAGA SHEKARA TA 2016 ZUWA 2026 DA ADADIN DUKIYAR DA TA LAƘUME A MANYAN GOBARAR DA AKA SANAR WA 'YAN JARIDU.

1) A shekara ta 2016  an samu tashin gobara sau ɗaya a kasuwar Sabon Gari, wato Abubakar Rimi Market sa ne Kano.

2) A shekara ta 2018, an samu tashin gobara a kasuwar Kurmi 'yan Gumama shaguna 77 ne suka ƙone ƙurmus.

3) A shekara ta 2019, ranar 6 ga Fabrairu shekara ta 2019 an samu tashin gobara a kasuwar 'yan Katako.

4)A ranar 10  ga watan Yuni a shekara ta 2019 an samu tashin gobara a kasuwar Ƙofar Ruwa shaguna 6 ne suka ƙone.

5) A ranar  14  ga watan Afrilu 2019 an samu tashin gobara a kasuwar Kurmi 'yan Nama inda shaguna 33 suka ƙone.

Tushe: Jaridar Daily Trust.
6) A watan Maris na shekara ta 2023 an samu tashin gobara a Kasuwannin Kano kamar: A Kasuwar Singa a Rumbunan ajiye kayayyakinsu. 

Sai a Kasuwar Kurmi inda ta ƙone shaguna 80.

An kuma samu gobara a kasuwar Abubakar Rimi inda ta ƙone shaguna 19 har da Masallacin kasuwar. Duka waɗannan gobarar sun faru ne a cikin mako ɗaya rak.

7) A watan Yuli na shekara ta 2023 an sake samun gobara a kasuwar Rimi inda ta ƙone shaguna guda 10.

8) A shekara ta 2024 an samu tashin gobara a kasuwar Kwari inda ta taɓa gidaje da dama. 

9) A shekara ta 2025 an samu tashin gobara a kasuwar Shuwaki inda ta ƙone rumfuna. 

10) A farkon watan fabarairu 2026 an samu tashin gobara a kasuwar 'yan Katako. 

11) A ranar Asabar da misalin ƙarfe 7 na yamma zuwa wayewar garin Lahadi, an samu tashin gobara a kasuwar Singa wadda ta laƙume dukiya mai ɗumbin yawa. 

Adadin yadda gobara ta tashi a kowace shekara, a shekaru goma da suka wuce. 

Shekara.        Sau. 
2016.                1
2018.                 1
2019.                 4
2023.                 4
2024.                1
2025.                1
2026.                2
Jumillar gobara a shekaru goma da suka gabata sun kai sau 14 a jihar Kano. 

Adadin ƙiyasin  dukiyar da aka yi asara a kowace gobara ta kowace shekara. 

Shekara            Naira
1. 2016 a kasuwar Sabon Gari an yi asarar da ta kai Naira tiriliyan biyu. 

2. A shekara ta 2023 a kasuwar Singa an yi asarar da ta kai naira biliyan biyar. 

3. A shekara ta 2024 a manyan kasuwannin Kano da aka yi gobara an yi asarar da ta kai naira biliyan ɗari. 

4. A shekara ta 2025 an samu asarar da ta kai sama da ta naira biliyan biyar a kasuwar Kantin Kwari. 

Sauran ƙananan kasuwannin Kano da aka yi gobara, an yi asarar da ta kai sama da biliyan goma. 

Jumilla daga shekara ta 2016 zuwa 2026 an yi asarar dukiya da ta kai naira tiriliyan 2 da biliyan 120, a tsawon shekara 10.

Wannan yakamata ku 'yan kasuwa ku samar wa da kanku mafita domin rage yawan asarar da kuke yi. 
Shawarwari:

1) Ku samar da gidan ruwa da hukumar kwana-kwana ga dukkan kasuwanninku, da za su ke ba wa kasuwanni ruwa da kashe gobara a duk lokacin da ya dace. Domin gwamnati, a nan ta gaza samar da motoci da ruwan da za a iya kashe maku gobara a duk lokacin da ta tashi. 

2) A samar da cibiyoyin ruwa a lungu da saƙon kasuwanninku don kare dukiyoyinku. Za ku ɗauki ma'aikata da za a tura hukumar kwana-kwana ta Kano su yi masu horo na musamman kan yadda za su ke kare maku dukiyoyinku babu dare babu rana. 
Abin da za ku kashe na kafa hukumar da gidan ruwan da albashin duka ma'aikatan, ba zai kai adadin dukiyar da kuka yi asara ta shekara goma ba, kuma kasuwanninku za su kasance cikin tsari.

Dole a sama wa kowace kasuwa hanya da za a iya shiga ta gaggawa idan buƙatar hakan ta taso, Mafi yawanku wayayyu ne, kuna fita kuna ganin kasuwanni a wasu ƙasashen, ba irin tsarin naku ba ne ba, ta yadda ake cike hanya da  shirya kaya a kan hanya. Dole a gyara domin a gudu tare a tsira tare. 

Allah ya kiyaye gaba. 
Ya mayar maku da abin da aka rasa. Amin. 
Jamilu Shuaibu Usman 
16 ga watan Fabarairu 2026.

Post a Comment

Previous Post Next Post