Trump Ya Gabatar da Jawabin State of the Union Mafi Tsawo, Ya Tabo Batutuwan Tattalin Arziki, Haraji da Rikice-rikicen Duniya

Shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump, ya kafa tarihi da gabatar da jawabin State of the Union mafi tsawo a tarihin ƙasar, wanda ya ɗauki kusan awa ɗaya da mintuna 50.

A cikin jawabin, ya mayar da hankali kan batutuwa masu muhimmanci da suka haɗa da harajin shigo da kaya (tariffs), tattalin arziki, shige da ficen baƙi, da kuma batun shirin nukiliyar Iran.

Trump ya kuma sake jaddada iƙirarinsa na cewa ya kawo ƙarshen yaƙe-yaƙe guda takwas tun bayan dawowarsa kan karagar mulki a bara, ciki har da rikicin da ke tsakanin India da Pakistan.

Shugaban ya gabatar da jawabin ne ga haɗaɗɗiyar zaman Majalisar Dokokin Amurka a zauren Majalisar da ke ginin US Capitol, a birnin Washington, a ranar Talata, 24 ga Fabrairu, 2026. Jawabin ya ɗauki awa ɗaya da mintuna 47, inda ya fara da cewa: “Ƙasarmu ta dawo—ta fi girma, ta fi kyau, ta fi wadata kuma ta fi ƙarfi fiye da kowane lokaci a baya.”

Wannan ne jawabin State of the Union na farko a wa’adinsa na biyu, kuma ya zo ne a wani muhimmin lokaci da United States Supreme Court ta soke dokar harajin gaggawa na duniya da ya ƙaddamar.

Haka kuma, jawabin ya gabaci zaɓukan tsakiyar wa’adi (midterm elections) da ake sa ran gudanarwa a watan Nuwamba mai zuwa, inda batutuwan tattalin arziki da manufofin ƙetare suka mamaye sahun gaba a ajandar siyasar ƙasar.

Post a Comment

Previous Post Next Post