Koriya Ta Arewa Ta Ce Ta “Girmama” Zabin Iran Na Mojtaba Khamenei A Matsayin Jagora

 Gwamnatin North Korea ta bayyana cewa tana girmama zaɓin da jama’ar Iran suka yi na naɗa Mojtaba Khamenei a matsayin sabon jagoran ƙasar (Supreme Leader). 

North Korea

A cikin wata sanarwa da kakakin ma’aikatar harkokin wajen ƙasar ya fitar ta kafar labarai ta gwamnati, an ce Pyongyang tana girmama ‘yancin jama’ar Iran na zaɓar jagoransu, bayan majalisar Assembly of Experts ta zaɓi Mojtaba Khamenei domin ya gaji mahaifinsa Ali Khamenei. 

Sanarwar ta kuma yi Allah-wadai da hare-haren da Amurka da Isra’ila suka kai kan Iran, tana mai cewa irin waɗannan hare-hare suna lalata zaman lafiya a yankin tare da ƙara haddasa rashin kwanciyar hankali a duniya. 

A cewar jami’an Koriya ta Arewa, duk wani yunƙuri na katsalandan a tsarin siyasa ko cikin harkokin cikin gida na Iran ya kamata a yi Allah-wadai da shi, domin yana tauye ikon ƙasar da ‘yancin jama’arta. 

Wannan matsayi na North Korea ya nuna ci gaba da kusanci tsakanin Pyongyang da Tehran, musamman a yayin da rikici ke ƙaruwa a Gabas ta Tsakiya. 

Post a Comment

Previous Post Next Post