Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ce ƙasarsa na da isassun makaman yaƙi da za a iya amfani da su “har abada”, yana mai jaddada cewa Amurka a shirye take ta yi nasara a duk wani rikici.
Trump ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa a dandalin sada zumunta na Truth Social, inda ya yi magana kan abin da ya kira tarin makaman da Amurka ke da su.Ya rubuta cewa, ana iya gudanar da yaƙe-yaƙe na dogon lokaci ta amfani da irin waɗannan makamai kaɗai.
Ya kuma ƙara da cewa, “Amurka na da tarin makamai marasa iyaka, kuma a shirye take ta yi nasara babba,”.
Trump ya kuma zargi tsohon shugaban ƙasar, Joe Biden, da bai wa Ukraine makaman Amurka masu matuƙar ƙarfi da yawa.
A ƙarshen wa’adin mulkinsa na shtekara huɗu, Biden ya amince Ukraine ta yi amfani da makamai masu linzami na dogon zango irin su ATACMS, waɗanda ke iya kai hari har nisan mil 190, kimanin kilomita 300.