Trump Ya Ce Dole Amurka Ta Shiga Wajen Zaben Sabon Jagoran Iran

 Shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa dole ne Amurka ta kasance cikin waɗanda za su taka rawa wajen zaɓen sabon jagoran addini mafi girma na Iran bayan mutuwar tsohon jagoran ƙasar, Ali Khamenei. Trump ya yi wannan furuci ne yayin wata hira da manema labarai, inda ya ce ba za a bar batun zaɓen sabon jagoran Iran ba tare da Amurka ta sa ido ko ta shiga cikin lamarin ba.

zaɓen sabon jagoran addini mafi girma na Iran

Trump ya kuma nuna adawarsa ga yiwuwar ɗan tsohon jagoran, Mojtaba Khamenei, ya gaji mahaifinsa. Ya ce wannan ra’ayi “ba abin karɓa ba ne,” yana mai jaddada cewa dole ne sabon jagoran Iran ya kasance wanda zai kawo sauyi a manufofin ƙasar, ba wanda zai ci gaba da tafiyar da tsoffin manufofi ba.

Sai dai a tsarin siyasar Iran, Amurka ba ta da ikon shiga cikin zaɓen jagoran ƙasar. A cewar dokokin ƙasar, majalisar malamai da ake kira Assembly of Experts ce ke da ikon zaɓar Jagoran Ƙoli (Supreme Leader). Wannan majalisa na da mambobi 88, kuma ita ce ke da alhakin zaɓar wanda zai gaji jagoran da ya rasu.

Masana harkokin siyasa sun ce kalaman Trump na nuna yadda Amurka ke son ganin an samu sabon shugabanci a Iran wanda zai kasance mai sassauci ko kuma wanda zai rage rikicin da ke tsakanin Iran da ƙasashen yamma, musamman a wannan lokaci da ake fama da tashin hankali tsakanin Iran, Amurka da kuma Israel.

Post a Comment

Previous Post Next Post