Iran Za Ta Yada Zango A Mexico Maimakon Amurika a Gasar Cin Kofin Duniya

'Yan wasan ƙasar Iran za su yi masauki ne a ƙasar Mexico yayin fafatawa a gasar cin kofin duniya (World Cup) da za a fara bugawa a ƙasar Amurika, a watan Yuni mai zuwa.

Ƙasar Amurika ta haramtawa ɗaukacin 'yan ƙwallon Iran matsuguni na dindindin a ƙasar tasu, hakan kuma ya samo asali ne, sakamakon yaƙin da ya ɓarke a tsakaninsu.

Hakan ya sa yanzu 'yan wasan Iran ɗin za su riƙa shiga Amurika ne su buga wasansu sannan su fito su dawo Mexico har zuwa ƙarshen wasan. 

Yaya kuke kallon wannan mataki?

Post a Comment

Previous Post Next Post