Tsohon Ministan Sufuri Na Najeriya, Rotimi Amaechi, Ya Gargadi Jam’iyyar ADC

 Tsohon ministan sufuri na Najeriya, Rotimi Amaechi, ya gargaɗi jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) cewa ba za ta iya ci gaba da sukar maguɗin zaɓe alhali kuma wasu daga cikinta na rubuta ko sauya sakamakon zaɓe ba.

Rotimi Amaechi

Amaechi ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa kan shirye-shiryen siyasar shekarar 2027, inda ya jaddada cewa dole ne jam’iyyun siyasa su kasance masu gaskiya da riƙon amana idan suna son jama’a su amince da su.

Ya ce matsalar maguɗin zaɓe a Najeriya ba ta taƙaitu ga jam’iyya ɗaya kawai ba, yana mai cewa duk wani ɗan siyasa ko jam’iyya da ke anfani da tsarin maguɗi ba su da hurumin yin korafi idan aka yi musu irin hakan.

Amaechi ya kuma yi kira ga jam’iyyun adawa da su mayar da hankali kan gina sahihin tsarin dimokuraɗiyya maimakon anfani da hanyoyin da suke zargi wasu da aikatawa.

Kalaman nasa sun tayar da muhawara a harkokin siyasar Najeriya, musamman yayin da ake fara shirye-shiryen zaɓukan 2027 da kuma ƙoƙarin jam’iyyun adawa na haɗa kai domin ƙalubalantar jam’iyyar APC mai mulki.

Masu sharhi kan siyasa sun bayyana cewa furucin Amaechi na nuna irin rikice-rikicen da ke ci gaba da addabar tsarin zaɓe a Najeriya, musamman batutuwan sahihancin sakamako da amincewar jama’a da tsarin dimokuraɗiyya.

Post a Comment

Previous Post Next Post