José Mourinho Ya Kulla Yarjejeniyar Koma wa Real Madrid

MADRID, Sifaniya — Shahararren mai horar da wasan ƙwallon ƙafa na ƙasar Fotigal, José Mourinho, ya riga ya sanya hannu kan kwangilar zama sabon manajan ƙungiyar Real Madrid.

Rahotanni daga amintaccen ɗan jaridar nan na kafar The Athletic, David Ornstein, sun tabbatar da cewa, Mourinho zai karɓi ragamar horar da ƙungiyar a hukumance da zarar Shugaban Real Madrid na yanzu, Florentino Pérez, ya lashe zaɓen shugabancin ƙungiyar mai zuwa da za a gudanar a ranar 7 ga watan Yuni.

Wannan mataki ya janyo ce-ce-ku-ce a duniyar ƙwallon ƙafa, inda masana ke kallon hakan a matsayin gagarumin sauyi ga makomar ƙungiyar ta Real Madrid.

Post a Comment

Previous Post Next Post