Marco Rubio Ya Ce An Samu “Gagarumin Ci Gaba” a Tattaunawar Amurka da Iran Domin Kawo Karshen Yaki

 Sakataren harkokin wajen Amurka, Marco Rubio, ya bayyana cewa an samu “gagarumin ci gaba” a tattaunawar da ake yi tsakanin Amurka da Iran domin kawo ƙarshen rikicin da ya daɗe yana haddasa tashin hankali a Gabas ta Tsakiya. 

Marco Rubio

Rubio ya bayyana hakan yayin wata ganawa da manema labarai, inda ya ce akwai alamun cewa ana matsowa kusa da cimma wata yarjejeniya da za ta taimaka wajen rage rikicin da kuma buɗe mashigar ruwan Strait of Hormuz, wadda ke da muhimmanci sosai ga safarar mai a duniya. 

Shugaban Amurka Donald Trump ma ya bayyana cewa yarjejeniyar zaman lafiya da Iran “ta kusa kammaluwa,” yana mai cewa ana ci gaba da tattauna wasu bayanai na ƙarshe kafin a sanar da cikakken matsaya. 

Rahotanni sun nuna cewa daga cikin abubuwan da ake tattaunawa akwai tsagaita wuta na wani lokaci, sake buɗe mashigar Hormuz domin jiragen ruwa su riƙa wucewa yadda aka saba, da kuma tattaunawa kan shirin nukiliyar Iran da tarin uranium da take da shi. 

Sai dai jami’an Iran sun nuna cewa har yanzu akwai babban rashin yarda tsakanin ɓangarorin biyu, kuma ba a cimma matsaya ta ƙarshe ba. Wasu jami’an Tehran sun jaddada cewa Iran ba za ta yi sassauci kan wasu muhimman buƙatunta ba. 

Masana siyasa da tattalin arziki sun ce idan aka cimma yarjejeniya, hakan na iya rage tashin hankali a yankin Gabas ta Tsakiya tare da taimakawa wajen daidaita farashin mai da kuma dawo da kwanciyar hankali ga kasuwannin duniya. 

Post a Comment

Previous Post Next Post