NELFUND Ta Karyata Jita-jitar Dakatar Da Biyan Alawus Din Dalibai

NAJERIYA — Hukumar Ba da Lamunin Karatun Gaba da Sakandare ta Najeriya (NELFUND) ta yi fatali da rahotannin da ke yawo a shafukan sada zumunta, wadanda ke ikirarin cewa Gwamnatin Tarayya ta dakatar da biyan alawus-alawus na abinci da gudanar da rayuwa ga dalibai masu cin gajiyar shirin lamunin karatu.

A cikin wata sanarwa da Daraktan Tsare-tsaren Sadarwa na hukumar, Oseyemi Oluwatuyi ya fitar, hukumar ta bayyana wadannan wallafe-wallafe a matsayin na bogi, kirkirarru, kuma wadanda aka tsara su da gangan domin yaudarar jama'a da kuma janyo fargabar da ba bu bukatar ta a tsakanin dalibai da sauran masu ruwa da tsaki.

Sanarwar ta kunshe da cewa: "Hukumar NELFUND na son musantawa da kuma yin tir da kaka-gida game da rahotannin karya da ke yawo a dandalin sada zumunta, wadanda ke ikirarin cewa Gwamnatin Tarayya ta dakatar da biyan alawus din dogaro da kai na dalibai a karkashin tsarin lamunin karatu.

"Wadannan rahotanni, wadanda suka hada da sanarwar bogi da aka jingina wa NELFUND da kuma hoton shafin farko na jaridar The Nigerian Tribune wanda aka kera ta hanyar fasahar AI, gaba dayansu na boge ne. An kera su ne kawai don janyo fargaba, rudani, da rashin amon baki tsakanin masu cin gajiyar shirin da kuma baki dayan al'umma."

Hukumar ta NELFUND ta jaddada cewa babu wani umarni da ya fito daga Gwamnatin Tarayya ko daga hukumar kanta da ke bayarda umarnin dakatar da alawus din daliban.

Haka itama, ta fayyace cewa bayanan da ke yawo ba su fito daga kowace iriyar kafar sadarwa ta hukumar ba, ko kuma wata kafa ta gwamnati mai iko da hakan. Hukumar ta kuma tabo batun hoton jaridar da ke yawo, inda ta tabbatar da cewa ba na gaskiya ba ne.

Yayin da take sake jaddada matsayinta, hukumar ta bayyana cewa tana nan daram kan bakarta na ci gaba da raba lamunin karatun da alawus-alawus din dalibai kamar yadda doka ta ba ta iko, tare da gudanar da ayyukanta cikin gaskiya da rikon amana.

A karshe, an yi kira ga dalibai masu cin gajiyar shirin, masu ruwa da tsaki, da kuma baki dayan al'umma da su yi watsi da wadannan rahotanni na boge, sannan su dogara duka-duka kan sahihan bayanai da ke fitowa ta halastattun kafofin sadarwa na hukumar.

Post a Comment

Previous Post Next Post