Shekara Daya da Kashe DPO a Rano

Rikicin da ya faru a Karamar Hukumar Rano a Jihar Kano ya samo asali ne sakamakon mutuwar wani matashi mai gyaran babura bayan da wani Babban Jami'in 'Yan Sanda (DPO) mai suna CSP Baba Ali Muhammad ya yi masa dukan kawo wuka bisa zargin laifin da bai kai ya kawo ba..

Shugaban Yansanda

A ranar 25 ga watan Mayu 2025, Mutanen garin Rano ake Jihar Kano suka kashe DPO na Babban Ofishin ’Yan Sandan garin tare da banka wa ofishin wuta.

Wata sanarwar da kakakin rundunar ’yan sanda a Jihar Kano, S.P. Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar ta bayyana cewa tashin hankalin ya samo asali ne daga mutuwar wani wanda ake zargi da aka tsare.

Ya bayyana cewa an kama matashin ne bisa laifin tuka babur ba cikin ganganci kuma zargin yana yin haka ne bayan shaye-shayen ƙwayoyi.

Ya ce, a yayin da yake tsare, ya nuna alamun rashin lafiya inda aka kai shi babban asibitin Rano, inda ya mutu da safiyar ranar 26 ga Mayu, 2025, da misalin karfe 6:00 na safe.

A sakamakon gaka, wasu gungun fusatattun mutane suka dkai hari a hedikwatar ’yan sanda ta Rano, inda suka cinna wuta a wasu sassan ofishin, suka lalata motoci goma, sannan suka kona wasu biyu.

Post a Comment

Previous Post Next Post