Tarihin Bahaushen Sarkin Musulmi Sultan Abdullahi Burja na Daular Musuluncin Hausawan Kano

Mu sani, Sarakunan Hausawa su ne suka mayar da kasar Kano babbar cibiyar hada-hadar kasuwanci da tsantsar gudanar da addinin Islama a yammacin Afirka tun sama da shekaru 587 (1438-1452).

Sarkin Kano

Dama tun can dubban shekaru Hausawa kwararrun ’yan kasuwa ne da ke fatauci da kala-kala na sana’o’i babu adadi.

Wato idan kuka lura, duk kusan kabilu da kuka sani za ku same su da wata sana’a daya da aka san su da ita. Amma wayewar Hausawa tun shekaru aru-aru ta wuce hakan.

Yau ya kamata mu ji wane Bahaushen Sarkin Kano nan Abdullahi ɗan Kanajeji, wanda aka fi sani da Abdullahi Burja.  

Wanda shi ne Sarki na 16 a jerin Sarakunan Hausawa na kasar Kano.

Sultan Burja, kwararren masanin kasuwanci ne, gwarzon jarumi, tsayayye, mai magana ɗaya. Adalcinsa, tausayinsa da amanarsa ya taimaka wajen bunkasa kasar Kano a fagen kasuwanci a ƙarƙashin yammacin Afirka.

Ta hanyar ƙulla kawance da ƙasashen makwabta da buɗe hanyoyin kasuwanci daban-daban, Abdullahi Burja ya sauya hanyar tafiyar da mulkin Kano da samar da hanyoyin kuɗin shiga zuwa kasuwanci da haɓaka kayan masarufi, abin da Kano da Hausawa suka shahara da shi a yau.

Saboda tsananin son shi da bunkasa kasar Hausawa… shi ne Sarkin Hausa na farko da ya kai ziyarar yarjejeniyar kasuwanci zuwa ƙasar Bornu.

Inda ya samu damar ƙulla yarjejeniya da Daular Bornu wadda ta ba da damar buɗe hanyar kasuwanci daga Gwanja zuwa Borno.

Sannan kuma, shi ne sarki na farko da ya shahara a kan mallakar raƙuma a ƙasar Hausa.

Wannan ƙoƙari na Bahaushen Basaraken ya sa… A ƙarshen ƙarni na 15, Kano ta zama ɗaya daga cikin manyan cibiyoyin kasuwanci a yankin ƙasar Hausa da ma yammacin Afirka baki ɗaya.

Duk ta hanyar wannan ciniki da harshen Hausa, addinin Musulunci da kyawawan al’adun Hausawa sun bazu a fadin yankin ta hanyar Hausawa malamai da ’yan kasuwa.

Abunka da Hausawa. Kun san duk inda Bahaushe ya dira sai mutanen suka amshi wasu al’adunsa saboda tsantsar amana da Hausawa ke da ita da kuma ƙwarewa da kyawawan al’adunsu, da son zaman lafiya da zamantakewa ba tare da nuna kabilanci ba, da tsantsar gaskiyarsu da aka yi musu shaida tun kafin zuwan Islama.

Sultan Abdullahi, sanadiyyar kasuwanci da ya buɗe tsakanin ƙasashen Hausa da ƙasar Gwanja ne ya sa malamai Hausawa suka rinƙa bin ayarin fatake zuwa sassa daban-daban na Afirka suna ƙara karatu suna kuma karantarwa.

Sanadiyyar hakan har suka samu gagarumar nasarar musuluntar da mutane da yawa a cikin ƙasar Gwanja, saboda kyawawan halaye da suke nunawa, da kuma yadda jama’ar ƙasar suka amince da su da shaidar da suka ba Hausawa ta amana da gaskiya.

Sunan mahaifiyar Abdullahi Burja shi ne Takida. Kuma shi ne ɗa na uku a jerin ’ya’yan Sarki Kanajeji da suka hau mulki a Kano.

A wata ƙissa a cikin ruwayar da aka nakalto bisa ga littafin tarihin Kano Chronicle, zamanin mulkinsa ya dace da ƙarshen mulkin wannan shahararriyar Bahaushiyar Sarauniyar nan ta binne Hausawan Zazzau wato Sarauniya Amina.

Shi ya yi mulki ne daga shekarar 1438 zuwa 1452.

Sultan Abdullahi Burja ta hanyar wani Galadimansa, ya gina sabbin garuruwa guda ashirin da ɗaya a kan hanyar kasuwanci, saboda tabbatar da tsaron lafiya da dukiyar al’umma masu zuwa kasuwanci kasar Kano.

Wannan tabbacin tsaron rayuka da kwanciyar hankali ya jawo hankalin jama’a, ciniki a Kano ya fara ƙarkata har zuwa ga manyan kayayyaki.

A lokacinsa an riwaito cewa dukkan ƙwararrun matasan Hausawa na Kano ana basu horon zama ƙwararrun dakaru soja na yaƙi saboda zama cikin shiri don baiwa ’yan kasuwan da ke zuwa kasuwanci kariya, sai dattawa ne kaɗai ake bari a cikin birni.

Sarkin Kano Abdullahi Burja, ya kafa wata sabuwar doka a kan masu tallan bayi maza da mata, ya ce su daina yawo suna wahalar da su, su daina dukan su wajen talla a cikin birni.

Sarki ya ce su rika fita can bayan gari kudu da tsohuwar Unguwar Mandawari, domin akwai manya-manyan bishiyoyi masu inuwa ko’ina a wurin, su rika zama suna saye ko sayar da bayi a gindin waɗannan bishiyoyi maimakon wahalar da ɗan Adam.

Littattafan tarihi duk sun tabbatar da ƙarfin yawan kyautar wannan Bahaushen Basaraken Sarki.

Sannan ya shahara a duniya da yadda yake da halin karimci.

A cikin littafin tarihin Kano mai suna “Kano Chronicle” an bayyana Sarki Abdullahi Burja a matsayin mai kyauta da karimci.  

Kuma yana ɗaya daga cikin shahararrun Hausawa da tarihi ba zai taɓa mancewa da su ba.

Domin yadda ya nuna zallar fasahar kakanni-kakanninsa Hausawa a kasuwanci da tsarin mulki don ciyar da ƙasa gaba, inda ya nuna gwaninta na yin yarjejeniyar kasuwanci don bunkasa ƙasa da kuma ciyar da ’yan baya su amfana.

Shi ne kakan-kakan Sarkin Kano mafi girma da shahara a tarihi wato Muhammadu Rumfa.

Ai tunda na ji na ji shi ne kakan Sarki Muhammad Rumfa, na ce ai ruwa baya tsami banza.

Ibrahim Gamji

Sources 

1. "Kano Chronicle"(Tarikh Arbab Hadha al-Bilad) – Translated by H.R. Palmer (1908)

2. "Government in Kano"(1350-1950)by M.G. Smith

3. "Studies in the History of Kano" (edited papers, Bayero University Kano)

4. "The Complete History of Kano" (999-1903)by Isaac Samuel

5. Kano in the Second Millennium: Selected Papers (Kano Millennium Conference papers)

Post a Comment

Previous Post Next Post