Nijeriya ta tura dakarun sojoji zuwa kasar Benin don yaki da ta'addanci

Babban hafsan sojin ƙasa na Najeriya, Waidi Shaibu, ya bayyana cewa Najeriya ta tura dakarunta zuwa jamhuriyar Benin  domin taimakawa wajen yaƙi da ta’addanci da sauran manyan laifuka da ke addabar yankin Afirka ta Yamma.

Sojin Nijeriya

Ya bayyana hakan ne a yayin taron shekara-shekara na hafsoshin rundunar sojin ƙasa da aka gudanar a Abuja, inda ya ce rundunar na ci gaba da haɗa kai da ƙasashen maƙwabta wajen musayar bayanan sirri da gudanar da ayyukan tsaro tare.

Shaibu ya ce tura sojojin zuwa Benin na nuna ƙudirin Najeriya na ƙarfafa tsaron yankin tare da dakile barazanar ‘yan ta’adda. Haka kuma ya yabawa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu bisa goyon bayan da yake bai wa rundunar soji ta fuskar inganta walwala, kayan aiki da ƙarfin aiki.

Ya ƙara da cewa an inganta kayan yaƙi, matsugunan sojoji, kula da lafiya da alawus-alawus domin ƙara wa dakarun ƙwarin guiwa wajen gudanar da ayyukansu.

A watan Disambar bara ne majalisar dattawa ta amince da bukatar Tinubu na tura sojojin Najeriya zuwa Benin domin taimakawa wajen tabbatar da zaman lafiya da kare dimokuraɗiyya bayan yunƙurin juyin mulki a ƙasar.

Post a Comment

Previous Post Next Post