Wani mutum mai shekaru 38 ya mutu bayan da wani babban farin kifin shark (great white shark) ya kai masa hari a jihar Western Australia, lamarin da ya tayar da hankali a yankin.
Rahotanni sun bayyana cewa harin ya faru ne da safiyar Asabar a kusa da Rottnest Island, wani shahararren wurin yawon buɗe ido da ke kusa da birnin Perth. Mutumin yana yin kamun kifi a ƙarƙashin ruwa tare da abokansa lokacin da kifin shark ɗin ya kai masa hari.
Jami’an tsaro sun ce an ciro mutumin daga ruwan tare da kai shi bakin teku domin ba shi agajin gaggawa, amma duk ƙoƙarin ceto rayuwarsa ya ci tura.
An kuma ruwaito cewa an ga wata babbar kifin shark mai tsawon kusan mita biyar a yankin kafin harin ya faru, lamarin da ya sa hukumomi suka gargadi jama’a da su yi taka-tsantsan yayin shiga ruwa a yankin.
Wannan hari na daga cikin hare-haren shark da suka janyo mutuwa a Australia a bana, yayin da hukumomi ke ci gaba da sa ido kan yankunan bakin teku domin kare rayukan masu yawon buɗe ido da masu wasannin ruwa.