A Wani Taro Da Aka Yi A Jigawa, Malaman Addini Na Arewacin Kasar Sun Amince Da Tinubu Ya Mamaita

A wani taro da aka yi a Dutsen jihar Jigawa, taron da ya tattara Malaman Addinin Musulunci 500 daga jihohi sha tara (19) na Arewacin ƙasar Nijeriya da Abuja, dukkansu sun goyi bayan Tinubu ya ci gaba da zama shugaban ƙasa har zuwa 2031.

Mai ba shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu shawara kan harkokin siyasa da sauran al’amura, Ibrahim Masari, ya ce kusan malaman addinin Musulunci da shugabannin addini 500 daga jihohin Arewa 19 da Abuja suka amince da sake tsayawa takarar Tinubu a zaɓen shugabancin ƙasar na 2027.

Masari ya bayyana hakan ne a lokacin da suke gudanar da taron Northern Muslim Intellectual Forum wanda aka gudanar a Dutse, Jihar Jigawa.

Ya bayyana cewa, mahalarta taron sun tattauna batutuwan da suka shafi, matsalolin tsaro da tattalin arziƙi da kuma abubuwan more rayuwa da ci gaban yankin Arewa, inda malaman suka bayyana gamsuwa da matakan da gwamnatin Tinubu ke ɗauka.

A cewar mai ba wa shugaban ƙasa shawara, mahalarta taron sun kaɗa ƙuri’ar amincewa da Tinubu tare da kira ga ‘yan Nijeriya, musamman al’ummar Arewa, da su goyi bayan sake zaɓensa da sauran ‘yan takarar jam’iyyar APC a 2027 daga sama har ƙasa.

Filin taron ya samu albarkar halartar gwamnonin jam'iyyar APC na Jigawa da Kano da Yobe da Sokoto da kuma Kaduna. Har wa yau, Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata, Barau I. Jibrin, da Ministan Gidaje, Alhaji Muttaƙa Rabe Darma sun samu halartar wannan gagarumin taro na farko, tun bayan da aka bayar da damar yin kamfen na zaɓen 2027 da za a yi nan ba da jimawa ba.

Post a Comment

Previous Post Next Post