Jami'an hukumar soji sun damƙe wani tsoho da matasa huɗu bisa zargin safarar kayaiyaki ga 'yan ta’adda a Borno
Dakarun Bataliya ta 18 na Rundunar Sojin Nijeriya da ke Borni sun cika hannu da wasu mutane biyar da ake zargin suna samar da kayayyakin ta'addanci da sauran kayan buƙatu ga ’yan ta’addan Boko Haram a Jihar Borno.
Sojojin sun kama mutanen ne da misalin ƙarfe 7:52 na daren Juma’a 21/08/2027, bayan da jami’ai masu sa ido da suke kula da na’urorin CCTV na sansanin sojojin suka hango su a gaban wani sansanin soja.
Rahotanni sun bayyana sunayen waɗanda aka kama da Umar Mohammed, mai shekaru 60 da Abubakar Goni, mai shekaru 42 da Abba Ali, mai shekaru 39 da Umaru Yusuf mai shekaru 30 sai kuma Ibrahim Bukar mai shekaru 30 shi ma.
Ko da sojojin masu kula da CCTV suka hango su, sai suka yi hanzarin tura jami’ai waɗanda suka yi nasarar damƙe mutanen biyar.
Da farko binciken ya nuna cewa hanyar da mutanen suka bi na daga cikin hanyoyin da ake zargin Boko Haram na amfani da su wajen jigilar kayayyakin tallafi, waɗanda suka haɗa da makamai da abinci da kuma sauran kayayyaki masarufi.
Yayin da ake tuhumarsu, waɗanda ake zargin sun bayyana cewa, wasu daga cikinsu ma’aikatan gawayi ne wasu kuma suna aikin ɗebo ’ya’yan kukar kwarba (baobab) ne.
Rahoton ya ci gaba da cewa, a halin yanzu rundunar sojojin na ci gaba da ƙoƙarin tantance mutanen da ake zargin, kafin daga bisani a miƙa su ga birged ɗin leƙen asiri ta soji ta 7 domin ci gaba da gudanar da bincike.
An bayyana cewa, wanna kamen yana daga cikin ayyukan leƙen asiri da sojojin ke ci gaba da gudanarwa domin gano tare da tarwatsa hanyoyin sadarwa da samar da kayayyaki ga ’yan ta’adda a yankin na Arewa maso Gabashin ƙasar.
Rundunar sojojin ta ce duk da cewa yanayin tsaro a yankin na ci gaba da kasancewa cikin kwanciyar hankali, akwai yiwuwar sauyin yanayi a kowane lokaci, yayin da dakarun ke ci gaba da kasancewa cikin shiri da ƙwarin gwiwar gudanar da ayyukansu.