Dino Melaye Zai Garzaya Kotu, Domin Jin Ba'asin Yadda Aka Sanya Sunan Ma'aikacin Gwamnati Cikin 'Yan Kwamitin Kamfen Na Shugaban Ƙasa Tinubu

Tsohon Sanatan Kogi Dino Melaye ya yi barazanar maka shugaban hukumar haraji ta ƙasa kotu, saboda samun gurbi a kwamitin kamfen na Tinubu

Tsohon Sanatan Kogi ta Yamma, Dino Melaye, ya ce zai maka Shugaban Hukumar Harajin Nijeriya (NRS), Zacch Adedeji, a kotu kan muƙamin da aka ba shi ba ɗaya daga cikin 'yan kwamitin kamfen na Shugaba Tinubu na jam'iyyar APC a zaɓen 2027 mai zuwa.

Dino, wanda yake cikin shugabannin jam’iyyar ADC a Kogi, ya ce akwai yiwuwar samun rikicin muradun aiki, ganin cewa Adedeji ma’aikacin gwamnati ne kuma an zo an naɗa shi Mataimakin Daraktan tara kuɗaɗen kamfen Tinubu.

Har wa yau, ya kuma soki matakin da Shugaba Bola Tinubun ya ɗauka na jagorantar kwamitin kamfen ɗinsa da kansa, yana mai cewa hakan na nuna rashin amincewa da wasu shugabannin APC.

Dino, ya ce a shirye yake ya garzaya kotu domin a tantance ko naɗin Adedeji ya dace da dokokin aikin gwamnati da ƙa’idojin ɗa’a na ma’aikatan gwamnati.

A jerin kwamitin kamfen da APC ta fitar, Tinubu ne Shugaban Kwamitin, yayin da Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima da Shugaban APC na ƙasa Nentawe Yilwatda suka kasance Mataimakan Shugabannin 'yan Kwamitin. An kuma naɗa tsohon Gwamnan Zamfara, Abdulaziz Yari, Darakta janar na kwamitin, yayin da Gwamnan Imo, Hope Uzodimma, ya zama Sakatare.

Gwamnan Ogun, Dapo Abiodun, shi ne Daraktan Tara Kuɗaɗen kamfen na kwamitin, yayin da Zacch Adedeji aka naɗa shi a matsayin mataimakinsa.

Post a Comment

Previous Post Next Post