Atiku Abubakar Ya Ba Wa Gwamnatin Jam'iyyar APC Amsar Yadda Zai Dawo Da Tallafin Man Fetur, Idan Ya Zama Shugaban Kasa

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, kuma ɗan takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar ADC, Alhaji Atiku Abubakar, ya ce dawo da tallafin man fetur a Nijeriya ba wani abu ba ne mai wahala. A wata fira da aka yi da shi, ya bayyana hanyoyin da gwamnatinsa za ta bi wajen aiwatar da hakan, muddin aka zaɓe shi shugaban ƙasa a zaɓen da za a yi shekarar 2027.

Atiku ya bayyana cewa, gwamnatinsa za ta riƙa samar wa matatun man fetur na Nijeriya ɗanyen mai a farashi mai rahusa, saboda su ma su riƙa sayar da man fetur a farashi mai sauƙi, domin isarsa ga al'umma, tare da ɗaukar tsauraran matakan tabbatar da cewa tallafin yana isa ga dukkan ’yan ƙasa, ba tare da ya sulale ta wata hanyar ba.

Ɗan takarar shugaban ƙasar ya ce, matuƙar ya zama shugaban ƙasa, dawo da tallafin ba wata babbar matsala ba ce, domin za a ware kuɗin tallafin ne a cikin kasafin kuɗin da ake yi a ƙarshen kowace shekara. Sannan a riƙa sanya ido tare da bibiyar kowace ganga ta ɗanyen man da aka samar, da kuma tabbatar da yadda ake kashe kuɗaɗen da aka ware.

Ya ƙara da cewa ba lallai tallafin ya kasance na dindindin ba, domin yayin da samar da man fetur a cikin gida ke ƙaruwa, za a iya rage tallafin a hankali a hankali har a kawo ƙarshen buƙatarsa, ba tare da an tsananta wa al'umma ba.

A cewar Atiku Abubakar, yin haka zai taimaka matuƙa wajen ganin an rage farashin man fetur da tsadar sufuri da ta abinci, tare kuma da ƙarfafa masana’antu da samar da ayyukan yi ga al'ummar ƙasa.

Post a Comment

Previous Post Next Post