Oyedele Ya Caccaki Masu Sukar Lamunin Bankin Duniya Ga Najeriya

Ministan Kuɗi kuma mai kula da tattalin arzikin Najeriya, Taiwo Oyedele, ya soki wasu ’yan Najeriya da suka rika sukar Bankin Duniya a shafukan sada zumunta kan bayar da rance ga ƙasar, yana mai cewa hakan ya nuna rashin fahimtar yadda tsarin hada-hadar kuɗi ke aiki.Oyedele ya bayyana hakan ne a Abuja yayin wani taron manema labarai kan ƙididdigar nasarorin da aka samu sakamakon gyare-gyaren tattalin arzikin Gwamnatin Tarayya.

Ministan ya ce wasu ’yan Najeriya sun yi amfani da shafukan sada zumunta na Bankin Duniya wajen zagi da sukar bankin saboda matakin da ya ɗauka na bai wa Najeriya rance. Ya ce lamarin ya yi tsanani har Bankin Duniya ya tilasta kashe damar yin tsokaci a shafukansa na sada zumunta.

Oyedele ya ce: “Mutane sun je shafin sada zumunta na Bankin Duniya suna zaginsa cewa yana bai wa Najeriya rance. Bankin Duniya sai ya kashe damar yin tsokaci. Mun samu rancen, domin ba haka tsarin yake aiki ba.”

Ya yi amfani da yadda na’urar cire kuɗi ta ATM ke aiki a matsayin misali domin bayyana dalilin da ya sa yake ganin wasu ’yan Najeriya ke sukar tsarin bayar da rance ba tare da fahimtar yadda tsarin yake aiki ba.

A cewarsa, mutanen da ba su fahimci yadda ATM ke aiki ba na iya ganin wasu suna cire kuɗi daga na’urar, sannan su yi kuskuren tunanin cewa tsarin yana fifita wasu mutane ne kawai.

Ya ce irin waɗannan mutane za su iya tara wasu su yi zanga-zanga har ma su lalata ATM, ba tare da fahimtar cewa dole ne a fara saka kuɗi a banki kafin a iya cire su ta ATM ba.

“Bayan sun lalata banki da ATM, tare da dukan mutane, har yanzu ba za su iya karɓar kuɗi ba, domin ba haka tsarin yake aiki ba,” in ji shi.

Ministan ya ce wannan ƙa’ida tana aiki iri ɗaya a harkokin tattalin arziki da tsarin kuɗi, yana mai jaddada cewa ya kamata ’yan ƙasa su fahimci yadda tsarin yake aiki kafin su rika sukar manufofin gwamnati.

“Idan ba ka fahimci yadda tsarin yake aiki ba, kana ɓata ƙarfi,” in ji Oyedele.

Ya ƙara da cewa fahimtar manufofin tattalin arziki da tsarin hada-hadar kuɗi zai taimaka wa ’yan Najeriya wajen bibiyar ayyukan gwamnati da kuma riƙe ta da alhakin abin da take yi.

Haka kuma, Oyedele ya yi gargaɗi kan amfani da bayanan tattalin arziki ta hanyar da ba ta dace ba domin cimma muradun siyasa. Ya ce wasu mutane na iya ƙoƙarin karkatar da alkaluman da ke cikin rahoton ƙididdigar gyare-gyaren tattalin arzikin gwamnati domin biyan buƙatun siyasarsu.

Ya buƙaci ’yan Najeriya da su yi la’akari da ko ayyukansu na taimakawa wajen gina ƙasa ne ko kuma raunana ta, yayin da gwamnati ke ci gaba da aiwatar da gyare-gyaren tattalin arziki.

An gudanar da taron ne ƙarƙashin taken “Nigeria’s Reform Scorecard: The Benefits and Harms Prevented”, biyo bayan umarnin Shugaba Bola Tinubu ga Ministan Kuɗi da ya fito fili ya bayyana nasarorin da aka samu, kuɗaɗen da aka kashe da kuma tasirin gyare-gyaren tattalin arzikin gwamnatin tun daga shekarar 2023.

Post a Comment

Previous Post Next Post