Amurka Ta Yi Barazanar Kakaba Sabbin Haraji Kan Brazil Saboda Manufofin Kasuwanci

 Gwamnatin shugaban ƙasar United States, Donald Trump, ta sanar da shirin ƙaƙaba sabon harajin kashi 25 cikin ɗari kan kayayyakin da ake shigowa da su daga Brazil, tana zargin ƙasar da amfani da manufofin kasuwanci na rashin adalci.

Brazil

Jami’in kasuwanci na Amurka, Jamieson Greer, ya ce shirin harajin na da alaƙa da damuwar Amurka kan dokokin kasuwancin dijital, kariyar haƙƙin mallakar fasaha, lalata muhalli ta hanyar sare dazuzzuka ba bisa ƙa’ida ba, da kuma wasu dokoki da Amurka ke ganin suna hana kamfanoninta cin gajiyar kasuwa a Brazil.

An bayyana cewa ana son amfani da Sashe na 301 na dokar kasuwanci ta Amurka wajen aiwatar da wannan mataki, wanda ke bai wa gwamnatin Amurka damar hukunta ƙasashen da take zargi da aiwatar da manufofin kasuwanci marasa adalci.

Sai dai rahotanni sun nuna cewa wasu manyan kayayyakin da Brazil ke fitarwa zuwa Amurka — kamar kofi, naman sa, makamashi, sassan jiragen sama, da wasu ƙarafa — na iya samun keɓewa daga sabon harajin domin rage tasirin matakin ga ‘yan kasuwa da masu amfani da kayayyaki a Amurka.

Matakin ya ƙara tsananta takun saka tsakanin Washington da Brasília, duk da cewa Amurka na samun ribar cinikayya da Brazil a ‘yan shekarun baya.

Shugaban ƙasar Brazil, Luiz Inácio Lula da Silva, ya soki shirin harajin, yana mai cewa akwai alamar siyasa a cikinsa. Ya kuma zargi magoya bayan tsohon shugaban ƙasa Jair Bolsonaro da ƙoƙarin jawo matsin lamba daga Amurka kan Brazil.

Rahotanni sun ce wannan rikici ya biyo bayan saɓanin da ƙasashen biyu suka yi a baya kan manufofin muhalli, tsarin kasuwanci, tsarin biyan kuɗi na dijital kamar Pix, da kuma batutuwan siyasa da suka shafi Bolsonaro.

Jami’an Amurka sun ce za a buɗe lokacin sauraron ra’ayin jama’a kafin a yanke hukunci na ƙarshe kan sabon harajin, tare da shirya zaman sauraro a watan Yuli.

Post a Comment

Previous Post Next Post