Abinci 7 Da Ke Taimakawa Wajen Rage Damuwa

1️⃣ Kifi mai kitse (Salmon, Sardine, Mackerel) Yana ɗauke da sinadarin Omega-3 wanda ke taimakawa rage kumburi a jiki da kuma tallafa wa lafiyar kwakwalwa, hakan na iya rage damuwa da tashin hankali.

 

Abinci

2️⃣ Ganyayyaki masu kore (Alayyahu da makamantansu) Suna da sinadarin Magnesium wanda ke taimakawa wajen kwantar da jijiyoyi da rage tasirin damuwa a jiki. 

3️⃣ Gyada da tsaba (Almonds, Pumpkin seeds, Chia seeds) Suna ƙunshe da Magnesium da sinadarai masu taimakawa kwakwalwa ta yi aiki yadda ya kamata lokacin damuwa.

4️⃣ Dark Chocolate Yana da antioxidants da flavonoids waɗanda za su iya taimakawa rage sinadaran damuwa (stress hormones) a jiki. 

5️⃣ Yogurt da sauran fermented foods Lafiyar hanji tana da alaƙa da lafiyar kwakwalwa. Yogurt na taimakawa inganta ƙwayoyin halitta masu amfani a hanji, wanda zai iya rage damuwa da tashin hankali.

6️⃣ Avocado Yana da Magnesium, fiber da lafiyayyun kitse waɗanda ke taimakawa rage cortisol (hormone na damuwa).

7️⃣ Koren shayi (Green Tea) Yana ɗauke da L-theanine, wani sinadari da ke taimakawa nutsuwa, rage tashin hankali da inganta mayar da hankali.

Post a Comment

Previous Post Next Post