An sasanta tsakanin Iran da Amurka, in ji Firaministan Pakistan

Ƙasar Pakistan mai shiga tsakanin Amurka da Iran a tattaunawar sulhu kan yaƙin da ƙasashen ke yi ta ce an cimma matsaya.

Firaministan Pakistan Shehbaz Sharif ne ya sanar da cewa an cimma matsaya ta ƙarshe tsakanin ƙasashen biyu, kamar yadda ya wallafa a shafinsa na X.

"A ƙoƙarin da Pakistan ke yi na shiga tsakani, muna sane da jita-jitar da ake yaɗawa domin lalata tattaunawar samar da zaman lafiyar da ake yi. Amma dai yanzu muna iya tabbatar da cewa an cimma matsaya ta ƙashe, kuma a yanzu haka Pakistan na aiki da duka ɓangarorin biyu domin kammala mataki na gaba," a saƙon da Mr. Sharif ya wallafa a shafinsa na X.

"Saura ƙiris a samu zaman lafiya," in ji shi.

Shi ma ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya wallafa cewa an kusa cimma matsaya da fahimtar da juna tsakaninsu da Amurka "kuma saura ƙiris".

Shugaban Amurka Donald Trump ma ya sake wallaga saƙon na Araqchi a shafinsa na X.

Post a Comment

Previous Post Next Post