An Tsinci Gawar Jami'in Kwastam A Jihar Bauchi

Wani babban jami’in hukumar kwastam ta Najeriya, Mista Lumi Elisha Gwamis, ya rasu, lamarin da ya jefa al’ummar gundumar Boi da ke karamar hukumar Bogoro a jihar Bauchi cikin jimami.

Jami'in Kwastam

Marigayin, wanda shi ne babban ɗan tsohon shugaban karamar hukumar Bogoro, Alhaji Elisha Tula Gwamis, ya rasu yana da shekara 44 a duniya.

Rahotanni sun nuna cewa wasu daga cikin mazauna yankin sun ce marigayin ya shafe wani lokaci yana fama da rashin lafiya da damuwa kafin rasuwarsa. Sai dai har yanzu babu wata hukuma da ta tabbatar da ainihin musabbabin mutuwar tasa.

Yayin wata ziyarar ta’aziyya da aka kai masa, mahaifin marigayin ya bayyana alhininsa kan rasuwar ɗansa, yana mai cewa Lumi yana cikin koshin lafiya kuma babu wanda ya yi tsammanin faruwar lamarin.

“Ɗana Lumi yana cikin ƙoshin lafiya. Ba mu san abin da zai faru ba sai da muka samu labarin rasuwarsa. Wannan babban rashi ne a gare mu,” in ji Elisha Tula Gwamis.

An shirya gudanar da jana’izar marigayin a ranar Laraba, 10 ga watan Yuni, a garin Boi.

A wani bangare kuma, Hukumar Kwastam ta Najeriya, reshen Federal Operations Unit (FOU) Zone D da ke Bauchi, ta musanta jita-jitar da ke yawo cewa jami’in ya kashe kansa.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, Umar Abdullahi, ya ce babu wani bayani a hukumance da ke tabbatar da irin waɗannan ikirari.

Ya bayyana cewa marigayin ya iso sashen ne bayan an canja masa wurin aiki daga tashar jiragen ruwa ta Tin Can Island, kafin daga bisani ya tafi hutun shekara da ya dace da shi.

Abdullahi ya ƙara da cewa hukumar ta samu labarin rasuwarsa ne daga mahaifinsa, yana mai jaddada cewa za su dogara ne kawai da sahihan bayanai da aka tabbatar, ba jita-jita ba.

Post a Comment

Previous Post Next Post