Ana Sa Toka Sa Katsi Kan Batun Rundunar Yan Sandan Nijeriya Da Al'umma Kan Batun 'yan Bijilanti Da Suka Wuce Wasu 'yan Sanda Suna Daga Masu Hannu

Rundunar 'yan sandan Nijeriya ta bayyana cewa, faifan bidiyon da yake ta yawo, wanda aka hango gomman mashina ɗauke da mutane bibbiyu a yankin ƙaramar hukumar Matazu, da suka zo suka wuce ma'aikatan 'yan sanda har suna ɗaga masu hannu alamun sannu ko barka da zuwa, ba ɓarayin daji ba ne, face 'yan bijilanti da suke taimakawa jami'an tsaron don ganin an murƙushe Kachalla Maha da masu taimakonsa.

Sai dai a zancen mazauna yankin suna cewa, waɗannan ɓarayin da aka gani yaran Alero ne da aka yi sasanci da su, gwamnati ta haɗa kai da su suke yaƙar Kachalla Maha a tare, kamar yadda Kachalla Maha ya yi iƙirarin an yaudare shi a wata firar da ya yi da shugaban ƙaramar hukumar Matazu.

Ko ma dai yaya abin yake. Shin kuna ganin gwamnati za ta ba wa 'yan bijilanti irin waɗannan makaman da suke ɗauke da su, wanda na tabbata 'yan sandan da ke tsaye a bakin titin ba su da irin su?

Post a Comment

Previous Post Next Post