APC Ta Dakatar Da Shugaban Jam'iyya Na Karamar Hukuma A Jihar Kebbi Saboda Zargin Zagon Kasa

Jam’iyyar APC a Jihar Kebbi ta dakatar da shugaban jam’iyyar na jihar, Abubakar Kana-Zuru, da kuma shugaban jam’iyyar na ƙaramar hukumar Zuru, Aliyu Abubakar Abiola, bisa zargin aikata ayyukan da suka saɓa wa manufofi da dokokin jam’iyyar.

Abubakar Kana-Zuru

A wata sanarwa da sakataren APC na jihar, Sa’idu Muhammad Kimba, ya sanya wa hannu, jam’iyyar ta ce matakin ya biyo bayan koke-koken da masu ruwa da tsaki a masarautar Zuru suka gabatar.

Sanarwar ta bayyana cewa an zargi jami’an biyu da nuna halin ko-in-kula ga harkokin jam’iyya, rashin mu’amala da masu ruwa da tsaki, rashin ƙwazo wajen wayar da kan magoya baya da kuma rashin bin ƙa’idoji da tsare-tsaren jam’iyyar.

Jam’iyyar ta ce ta ɗauki matakin ne bayan gudanar da binciken cikin gida kan zarge-zargen da aka yi musu.

APC ta sanar da dakatar da Abubakar Kana-Zuru daga matsayin shugaban jam’iyyar na jihar, inda ta ce mataimakin shugaban jam’iyyar na jihar zai riƙa gudanar da ayyukan ofishin a matsayin riƙo har sai an ba da wasu umarni.

Haka kuma, jam’iyyar ta dakatar da Aliyu Abubakar Abiola daga mukaminsa na shugaban APC a ƙaramar hukumar Zuru.

A wani mataki makamancin haka, gwamnatin Jihar Kebbi ta dakatar da kwamishinan raya kiwo da kamun kifi, Kabir Alaramma.

Sakataren gwamnatin jihar, Yakubu Bala-Tafida, ya bayyana cewa dakatarwar ta fara aiki nan take kuma za ta ci gaba har sai an bayar da wani sabon umarni.

Sanarwar ta kuma umarci Alaramma da ya miƙa dukkan kadarorin gwamnati, takardun aiki da sauran nauyin da ke hannunsa ga babban sakataren ma’aikatar har zuwa lokacin da za a ɗauki mataki na gaba.

Post a Comment

Previous Post Next Post