ASUU Na Kokarin Shiga Yajin Aiki Saboda Rashin Biyan Alawus

Kungiyar Malaman Jami'o'i ta Najeriya (ASUU) ta yi barazanar shiga yajin aikin sai baba-ta-gani a jami'o'in jihohi 11 idan gwamnatocin jihohin Edo, Delta, Ondo, Adamawa, Borno, Taraba da Yobe ba su aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma tsakanin gwamnatin tarayya da ASUU ta shekarar 2025 ba kafin ƙarshen watan Yuli.

ASUU

Shugabannin shiyyoyin Benin da Yola na ƙungiyar sun bayyana hakan a tarukan manema labarai daban-daban, inda suka ce gwamnoni sun gaza biyan alawus na CATA. sauran alawus-alawus da kuma bashin haƙƙoƙin malamai tun daga Janairun 2026.

ASUU ta ce rassanta a jami'o'in da abin ya shafa sun fara shirye-shiryen dakatar da dukkan harkokin karatu, tare da kira ga gwamnonin da su gaggauta aiwatar da yarjejeniyar da biyan dukkan basussukan domin kauce wa yajin aikin da ka iya kawo cikas ga harkokin ilimi.

Post a Comment

Previous Post Next Post