Matashin ɗan wasan tsakiya na Ingila, wanda yake taka leda a ƙungiyar Manchester United Kobie Mainoo, Wanda ya Sha fama da tsohon mai horas da ƙungiyar ta Manchester United Ruben Amorim a lokacin jagorancinsa, ya sake faɗawa mummunan hannu.
Tun bayan da mai horas da tawagar Ingila Thomas Tuchel ya kira Kobie Mainoo domin ya wakilci ƙasarsa, tare da taka leda a gasar cin kofin duniya da yake gudana a Amurka da Canada da kuma Mexico a wannan shekarar ta 2026. Mutane da yawa sun kasa haƙurin ganin yadda har yanzu Kobie Mainoo bai bayyana a cikin ko da wasa ɗaya daga cikin wasanni huɗu da suka buga ba.
A yau ne dai ƙungiyar ta doke ƙungiyar Dr Congo a mintinan ƙarshe na gasar zagaye 'yan 32, wanda hakan ya ba wa tawagar ta Ingila damar tsallakawa zuwa zagaye na 'yan 16.
Shin kuna ganin Kobie zai samu damar buga wasa a cikin tawagar ƙasarsa kuwa? Matuƙar Rice da Anderson na a cikin tawagar?
To wai me ya sa ma, sai Mainoo kaɗai ake tsegumi ba a sa wasan, ko dai kawai don ya fito daga ƙungiyar Manchester United ne?