A ci gaba da fafatawa a wasannin cin kofin duniya, na rukunin 'yan 32. Idan ba ku manta ba, ƙungiyoyin Afirka tara ne cikin goma suka samu damar tsallakawa zuwa wannan matakin bayan da aka kori ƙungiya ɗaya tun a karawar rukuni.
A wasannin jiya an cire ƙungiyoyin Afirka guda 3 Dr Congo wadda tawagar Turawan Ingila (England) ta yi ma yankan ƙauna a cikin mintina na 86 bayan da suka fara zura ƙwallo a ragar Ingilar, a ƙarshe dai wasan ya tashi 2 da 1 wanda hakan ya sa dole Dr Congo su koma 'yan kallo a gasar.
Sai kuma ƙungiyar Ivory Coast waɗanda Norway ta doke su a mintina na 86, bayan da wasan ya kasance 1 da 1 har zuwa wannan lokaci, sai a wannan mintinan komai ya sauya, Halland ya tattara wa Ivory Coast kayansu ya ce su nufo Afirka domin sake shiri kafin wasu shekaru 4 masu zuwa.
Senegal ta doke Belgium da ci 2 da nema 0 har a mintuna na 51, sai dai abin takaici ya zuwa mintinan 86 duka labari ya sauya salo, domin ya zuwa wannan lokacin wasan ya jagwale ya koma ɗanye, Belgium sun farke duka ƙwallayensu an koma 2 da 2. Daga cikin mintuna 30 da ake ƙarawa, a nan ne aka sake zura wa Senegal ƙwallo 1 wadda ta yi sanadiyyar ba wa Belgium ci gaba da fafatawa a rukunin 'yan 16, yayin da Senegal masu riƙe da kambun kofin Afrika suka harhaɗa ya nasu ya nasu suka bar gasar cin kofin duniya suka dawo gida.