An Sace Mutane 2 A Garin Tsuntsaye

A daren jiya Laraba 1/6/26 da misalin ƙarfe 9 na dare da 'yan mintina, wasu gungun ɓarayin daji sun shiga garin Tsuntsaye da ke kusa da Garu ta ƙaramar hukumar Musawa jihar Katsina, inda suka yi harbin gargaɗi ga mazauna garin, wanda hakan ya tilastawa al'ummar da ke waje suna fira komawa gidajensu ba tare da wani shiri ba.

Wannan shi ne karon farko da ɓarayin suka taɓa shiga garin Tsuntsaye, amma dai sun daɗe suna shiga makwabtansu Garu da 'Yar Kanya da kuma Ƙira.

A firar da na yi da mazaunin garin kan al'amarin, ya tabbatar min da cewa: "Da farko wani suka fara turowa a cikin garin yana tambayar gidan wani bawan Allah wanda suka ɗauke matarsa da 'yarsa. Bayan da suka gane gidan ne sai suka yi abin da suka yi, ba a jima ba kawai sai muka fara jin harbe-harbe har sau uku, daga nan fa, sai abin da ya faru ya faru. Ba mu samu natsuwa ba sai bayan da komai ya lafa, sannan muka tabbatar da sun tafi da Malama Ummi matar Alhaji Ummaru Maiwake wanda suka zo suna tambayar gidansa da kuma 'yarsa Ruƙayya."

Alhaji Ummaru Maiwake ba wani shahararren mutum ba ne a ƙaramar hukumar Musawa ba, sai dai yana daga cikin waɗanda Allah ya rufa ma asiri a ƙauyensu, mutum ne da yake sana'ar Arkomi (awo), daga baya an ce ya sayi mota yana kabu-kabu da ita, ba ma'aikaci gwamnati ba ne, bai kuma tara wasu maɗuɗan kuɗaɗe ba.

Ya zuwa yanzu dai da ake rubuta wannan rahoton, ba a samu rahoton wani da ya ji rauni ko mutuwa ba, sai dai waɗancan matan biyu da aka yi gaba da su. Kuma har yanzu ba a gama tabbatar waɗanda suka kawo harin ba, domin ya zuwa yanzu babu wanda ya ɗauki alhakin kawo harin.

Sai dai ana ƙarfafa zargi a kan yaran Kachalla Muhammadu domin yankinsa ne kuma a bayabayan nan Kachalla Muhammadu a cikin wata waya da suka yi da Kwamred wadda ta karaɗe soshal midiya, ya tabbatar wa da al'umma cewa zai zafafa hare-harensa tare da kama manyan mutane a kan hanyar Gidan Mutum Ɗaya da Rimaye da sauransu, matuƙar ba a sakar masa yaransa Aminu da Nasiru da dabbobinsa da aka kama a Jikamshi ba, ba a sani ba ko shi ne ya fara cika alƙawari.

Muna addu'ar Allah ya kuɓutar da waɗannan bayi nasa ya kuma kawo mana zaman lafiya a yankunammu.


Post a Comment

Previous Post Next Post