Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya amince da kafa wani kwamiti na musamman domin yaƙi da shaye-shayen miyagun kwayoyi da safarar haramtattun kwayoyi a jihar.
Mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis.
An nada tsohon shugaban Hukumar Karɓar korafe-korafe da yaƙi da cin hanci ta Kano, Muhuyi Magaji Rimingado, a matsayin shugaban kwamitin.
Kwamitin ya kunshi wakilai daga hukumomin tsaro da na lafiya da suka hada da NDLEA, DSS, ‘yan sanda, NSCDC, Hukumar Kwastam, Hukumar Shige da Fice, Hukumar Hisbah ta Kano, Majalisar Malamai da kuma wasu kwararru da masu ruwa da tsaki.
Gwamnatin jihar ta ce an kafa kwamitin ne domin hada kai tsakanin hukumomi wajen dakile safarar miyagun kwayoyi, gurfanar da masu laifi cikin gaggawa da kuma rage yawan masu amfani da kwayoyi ta hanyar fadakar da al’umma.
An kuma dora wa kwamitin alhakin tattara bayanan sirri, gano cibiyoyin safarar kwayoyi, gudanar da samame, kamo masu laifi da kuma bada shawarwari kan kwace kadarorin da ake zargin suna da alaka da harkar miyagun kwayoyi.
Bugu da kari, kwamitin zai gudanar da yakin wayar da kai musamman ga matasa da dalibai, tare da hada kai da cibiyoyin addini da na gargajiya domin tallafawa masu fama da matsalar shaye-shaye.
Gwamna Yusuf ya bayyana cewa shan miyagun kwayoyi na daga cikin manyan barazanar da ke fuskantar makomar matasan jihar, yana mai jaddada kudirin gwamnatinsa na amfani da dukkan hanyoyin da suka dace wajen magance matsalar.
Ya kuma bukaci mambobin kwamitin su gudanar da aikinsu cikin gaskiya, kwarewa da kishin kasa domin kare makomar Jihar Kano.
